“idan bamu rage gurbatacciyar iskar da ake fitarwa ba yanzu, zamu sami mutane miliyan dari da zasu yi rayuwa cikin talauci nan da shekara ta dubu biyu da talatin,” inji babban jami’in kula da dumamar yanayi na bankin duniyan a hirarshi da kamfanin dillancin labaran Faransa.
Tallafin da za a yiwa kasashen dake fama da talauci su iya rayuwa a yanayi mai zafi da kuma yanayi mai matukar tsanani zai hada da gina gidaje masu karko, da samar da hanyar samun ruwan sha mai tsabta, da kuma abinda bankin ya kira, “hanyar noma mai inganci.
Sanarwar bankin tazo ne a daidai lokacin da ake fara taron makonni biyu da ya hada kan kasashe dari biyu kan dumamar yanayi a birnin Katowice, na kasar Poland.
Facebook Forum