Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Gano Wata Cutar Dake Shanye Bangaren Jikin Yara


Yara a Amurka
Yara a Amurka

Yawan kananan yaran da suka kamu da wata cuta mai shanye jiki yayi yawan da ba a taba gani ba a Amurka. A cewar hukumar hana yaduwar cututtuka ta CDC.

Jiya Litinin hukumar CDC ta tabbatar da cewa an sake samun sama da yara 24 sun kamu da wata cuta mai kamar Polio da ake kira Acute flaccid myelitis AFM, wanda hakan ke nuni da cewa an samu yara 158 a jihohi 36 na Amurka cikin wannan shekarar.

Jami’an lafiya a Amurka har yanzu sun kasa gano abin da ke haddasawa kananan yara su rasa damar iya juya fuskarsu da wuyansu da bayansu da hannayensu da kuma kafafunsu. Alamomin cutar na bayyana ne kusan mako guda bayan yara sun yi zazzabi ko wata cuta mai shafar numfashi.

Ana alakanta wannan cuta da cewa cutar Polio ce, amma jami’an lafiya sunce babu wata shaida da ke nuna cewa cutar AFM tana da alaka da Polio, wadda aka kawar da ita a Amurka bayan da aka sami alurar riga kafinta tun shekarar alif 1950.

Hukumar CDC na bibiyar cuttuttuka da suka shafi AFM tun watan Agustan 2014. Tun lokacin, an tabbatar da samun yara 484 da suka sami cutar AFM, a cewar hukumar lafiya.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG