Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fadar Shugaban Amurka Ta Yi Watsi Da Gargadin Sauyin Yanayi


Gwamnatin Amurka karkashin Shugaba Donald Trump na kokarin rage muhimmancin rahoton nan da aka fitar wanda ya kunshi gargadi mai tsanani kan abin da ka iya faruwa sanadiyyar canjin yanayi a Amurka.

Fadar Shugaban Amurka ta White House ta ce akasari rahotan ya ta'allaka ne kan abin da fadar ta kira, "wasu hasashe masu tsanani" wadanda ba su yi la'akari da sabbin fasahohin zamani da wasu 'yan dabarun da ake amfani da su wadanda za su rage gurbata muhalli da iskar carbon ke yi da kuma illa ga muhalli.

Shirin Amurka na Binciken Canji a Duniya, na US Global Change Research, wanda hadaka ce ta ma'aikatu da cibiyoyi wajen 13, ya gabatar da kashi na hudu na sakamakon bincike kan canjin yanayin, wanda kwararru wajen 300 su ka harhada, ya yi hasashen cewa irin wadannan bala'o'in za su karu kuma za su dada yin tsanani muddun ba a dau matakai na kare tattalin arzikin Amurka da muhalli da lafiyar jama'a da kuma walwalar jama'a cikin shekaru masu zuwa ba."

Mai magana da yawun fadar ta White House Lindsay Walters ta kara cewa tun zamanin tsohon Shugaban Amurka Barack Obama aka fara harhada wannan bayanin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG