Tun a watan Satumba ne ake ta fuskantar hare-haren ‘yan kungiyar Boko Haram, da suke kaiwa kan jama’a da ma sansanonin ‘yan gudun hijira da kuma cibiyoyin jam’an tsaro, wanda yayi sanadiyar rayuka masu yawa.
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya yi ta gudanar da taro da shugabannin jami’an tsaro kan hanyoyin da za a bi wajen ganin an magance matsalar.
Sai dai kuma al’ummomin jihar Borno sun fito domin sake tunatar da shugaban kasa da ma sauran masu kula da alhakin tsaro a kasar, sake tashi tsaye.
Yanzu haka dai al’ummar Najeriya sun saka ido domin ganin irin matakan tsaron da shugabannin zasu dauka, don kawo karshen hare-haren ‘yan kungiyar Boko Haram.
Domin karin bayani saurari rahotan Haruna Dauda.
Facebook Forum