Babban hafsan hafsohin sojojin Najeriya, janar Tukur Buratai, ya yi jawabi a babban birnin Abuja, wajen wani taron bita da aka shiryawa dakaru, jawabin da ya janyo cece-kuce.
Rundunar sojojin Najeriya shiyya ta bakwai dake garin Maiduguri, ta mika wata ‘yar bautar ‘kasa da ‘yan kungiyar Boko Haram su ka sace ga gwamnatin jihar Borno.
Amurka ta ce zata iya tabbatarwa jiragen ruwa dake kai-komo tsakanin tekun Peshan da tekun Oman babu wata matsalar sufuri kuma zata yi hakan ne ta hanyar diflomasiya ko kuma ta amfani da karfin soja, inda take ci gaba da kalubalantar Iran cewa itace ta kai hari a kan jiragen dakon mai a kan tekun.
Firai ministan kasar Libya da duniya ta amince da shi yace ba zai wata tattaunawa ba da abokin gabarsa a kan batun mulkin kasar.
Titunan kasar Hong Kong sun sake cikewa makil da dubban daruruwar masu zanga zanga saye da babbakun kaya a jiya Lahadi domin kalubalantar kudirin nan da zai bada dama a mika masu laifi ga China.
Kasar Kamaru ta ce mayakan ‘yan a ware sun kashe ‘yan sanda hudu su ka kuma raunata shida a garin Eyumojock da ke sashin kudancin kasar na bangaren ‘yan Ingilishi.
An kama daruruwan magoya bayan shguaban ‘yan adawa Kamaru, Maurice Kamto, wanda ke fuskantar zargin cin amanar ‘kasa bayan da ya jagoranci zanga-zanga da yin imanin shine ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan Oktoba.
Kungiyar Tarayyar Afirka, ta ce ta dakatar da dukkan wata hulda da kasar Sudan, har sai an kafa sabuwar gwamnatin farar hula.
Kasar Mexico tayi gargadi ga shugaban Amurka Donald Trump akan barazanar da shugaban ya yi na labta wa kayan Mexico da suke shiga Amurka Haraji, inda take cewa wannan zai iya kawo illah ga kasashen biyu.
Hukumomi a kasar Kamaru sun kara tsaurara matakan tsaro a yankin matatar man kasar, biyo bayan wata fashewar bututun mai da ya faru a karshen mako, wanda yayi sanadiyar rufe matatar.
Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya yi Allah wadai da harin da jami’an tsaron Sudan suka kai jiya Litinin domin tarwatsa masu zanga-zanga a birnin Khartoum, inda suka kashe tare da jiwa mutane dayawa rauni.
Yau Talata ranar hudu ga watan Yuni tazo daidai da ranar ‘daya ga watan Shawwal, ranar da ake karamar sallah a Najeriya.
A daidai wannan lokaci da ake haramar sallar azumi, yanzu haka hukumomi tsaro a jihohin Adamawa da Taraba sun kara baza jami'ansu don tabbatar da an gudanar da bukukuwan cikin kwanciyar hankali ba tare da fargaba ba.
Amurka ta shirya ba tare da wani sharadi ba ta tattaunawa da Iran domin kawo karshen tankiya tsakanin kasashen biyu, inji sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo a jiya Lahadi, amma kuma ya bayyana shakku ko Tehran zata amince da wata sabuwar tattaunawa.
Wani farmaki ta sama da Isra’ila ta kai a kan tungar sojin Syria ya kashe soja daya kana ya raunata wasu biyu, ya kuma lalata wani ma’ajiyin makamai, a cewar ma’aikatar labaran kasar Syria.
Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar mazabar kudancin Borno Sanata Mohammed Ali Ndume, ya ce ya kamata shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ajiye duk wani batu dake gabansa ya fuskanci matsalar tsaro kawai.
Hukumomi a gabashin Congo sun ce akalla mutane talatin sun mutu kana wasu mutane dari biyu sun bata bayan wani jirgin ruwa ya nutse a wani tafki.
Domin Kari