Anji karan fashewa tare da harba-harben bindiga lokacin da jami’an tsaron suka afkawa masu zanga-zangar a kofar ma’aikatar tsaro, inda masu zanga-zanga suka shafe watanni takwas suna neman Sojoji su mika mulki ga farar hula.
Shaidu sunce kafin yamma, an kore kowa daga wajen.
Kwamitin likitocin Sudan, wadanda suka bar aiki saboda zanga-zanga, yanzu sunce yawan mutanen da suka mutu ya kai 30, wasu dayawa kuma sun raunata.
Shugabar hukumar kare hakkin bil Adama ta MDD Michelle Bachelet, itama ta yi Allah wadai da harin, ta kuma yi kira ga jami’an tsaron da su dakata cikin gaggawa.
Facebook Forum