Kalaman shugaban Amurka Donald Trump da mai bashi sahawara a kan tsaron kasa John Bolton a kan barazanar shirin makaman nukiliyar kasar Korea ta Arewa sun bambanta da juna.
Kananan jami’iyyu a Turai suna samun karin goyon baya a zaben gama gari na Majalisar Dokokin nahiyar Turan, zaben da ‘yan siyasa da masu sharhi ke ganin ka iya zama mafi muhimmanci tun shekarar 1979, lokacin da Kungiyar Tarayyar Turai ta fara gudanar da zaben ‘yan Majalisar nahiyar.
Ya yin da ya rage kwanaki biyu sabbin gwamnoni a Najeriya su karbi ragamar mulki, yanzu haka an soma cece kuce game da gwamnatocin jihohin da ke shudewa da kuma bangaren sabbin gwamnoni game da basusunka da aka bari.
Gwamnatin jihar Zamfara mai barin gado ta Abdul’aziz Yari ta ce ta amince da sakamakon hukuncin kotun koli da ya aiyana kuri’un ta a matsayin marar sa amfani.
Yanzu dai dan takarar babbar jam’iyyar adawa PDP a jihar Zamfara Bello Matawallen Maradun ya zama sabon gwamnan jihar Zamfara.
Kasar Bahrain da Amurka sun fada a jiya Lahadi cewa zasu shirya taro mai taken zaman lafiya zuwa ga ci gaba a cikin watan Yuni domin farfado da harkokin tattalin arziki Falasdinu, indai har za a cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Falasdinawa da Isra’ila.
‘Yan kasar Sudan sun caccaki wakilin Amurka a kasar saboda yin liyafa tare da daya a cikin mutane da ake musu kallon masu ruruta yaki a kasar.
Shugaban Amurka Donald Trump ya yiwa Iran kashedi da kakkausar murya, yana mai barazanar fatattakarta idan ta kaiwa Amurka ko kuma kawayen Amurka hari.
Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta fada jiya Lahadi cewa sake jibge rundunar sojin Houti a wasu muhimman hanyoyin shiga Yamal ya yi daidai da tsarin da aka tabbatar.
Amurka ta fada a jiya Lahadi cewa tana sa ran China za ta maida martani wurin kara haraji a kan kayyakin da Amurka ke aikawa China, biyo bayan karin haraji da shugaba Donald Trump ya yi a kan kayayyakin China da za a shigo dasu nan Amurka.
‘Yan sanda a wata unguwar nan Washington suna farautar wanda ya kashe Bettie Jennifer, uwargidan wani shahararren dan wasan fina finai a Ghana Chris Attoh.
A kokarin neman mafita kan matsalolin tsaro a shiyar Arewa maso Gabashin Najeriya, hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya ta bada horo na musamman wa wassu ‘yan kato da gora.
Wata karamar kotun soja a Algeria ta ce an gudanar da bincike a kan wani dan uwa kuma na hannun daman shugaba Abdelaziz Bouteflika da wasu manyan sojoji biyu da suke jagorantar sashen leken asirin kasar a baya a kan cin amanar kasar kuma an daure su a gidan yari.
Shugaba Donald Trump ya fada a jiya Lahadi cewa kada mai bincike na musamman Robert Muller ya bayyana gaban majalisar ya bada bahasi, lamarin da ya sabawa matsayar shugaban ta baya cewa ya bar wannan sahawarar ga Antoni janar.
An kashe akalla mutane 40 a wani hatsarin jirgin saman daukar fasinja samfurin Sukhoi Superjet-100 da ya kama da wuta ya yin da yake sauka a wani filin saukar jirage na birnin Moscow a jiya Lahadi.
An umarci ‘yan Najeriya da su tashi da azumin watan Ramadan ranar Litinin.
Kananan yara a kasar Ghana sun fara karbar wata allurar rigakafin da aka yi domin kawo karshen zazzabin cizon sauro da ake kira Maleriya.
Domin Kari