Anyi kamen ranar Asabar lokacin da jami’an tsaro suka tarwatsa zanga-zangar neman a sako kamto.
Germain Kamte wata mai sayar a litattafai ce, da aka samota kwance cikin mawuyacin hali ranar Litinin a unguwar Nionkak dake babban birnin Kamaru, baki daya jikinta a gurgurje.
Ta fadawa wadanda suka samota cewa ‘yan sanda ne suka tsayar da ita da abokanta hudu, suka kuma zargesu da goyon bayan zanga-zangar da aka shirya, sannan suka yi musu dukan tsiya.
‘Yan sandan Kamaru sun ki yin magana kan zargin da kamte ta ke musu, amma yawancin lokuta suka kan yi watsi da maganar cewa suna amfani da karfin da ya wuce ‘kima.
Paul Atanga, dake zama ministan ma’aikatar kula yankuna, ya ce an aika da ‘yan sanda ne domin su samar da zaman lafiya.
Ya kuma ce zanga-zangar da jam’iyyar adawa ta shirya ta sabawa doka, kuma shugabanta da aka kama Maurice kamto, barazana ne ga zaman lafiya.
Magoya bayan kamto sun yi alkawarin yin watsi da dokar hana zanga-zanga ranar Asabar, sun kuma fito sunyi domin a sake shi cikin gaggawa, tare da magoya bayansa sama da 500 da aka kama ake tsare da su.
Amma jami’an tsaron Kamaru sun tarwatsa zanga-zangar, suka kuma kama kusan mutum 200 magoya shguaban adawar, a cewar jam’iyyar CRM.
Sakataren jam’iyyar adawa ta CRM Christopher Ndong, ya yi Allah wa dai da yadda hukumomi suka aika da dakarun kasar domin suka kama tare da hana mutane ‘yancinsu na yin zanga-znaga.
Ga ci gaban fassarar rahoton Moki Edwin Kindzeka daga birnin Yaounde:
Facebook Forum