Kungiyar kwallon kafar Arsenal ta shirya sayar da dan wasan tsakiya Thomas Partey a lokacin buda kasuwar cefanen ‘yan wasa ta bazara, bisa sha’awa da wasu kungiyoyin Saudi Arabia suka nuna kan dan wasan.
Asamoah Gyan ya kawo karshen wasar kwallon kafa, bayan kafa tarihin zama dan wasar kasar Ghana da ya fi kowa yawan zurawa kasar kwallo a raga, kuma dan wasan da ke kan gaba a Afrika wurin yawan zura kwallo a gasar cin kofin duniya.
Palacas Negras da ke shirya kece reni da ‘yan wasan Black Stars na Ghana a wassanin neman gurbin shiga gasar cin kofin Afrika, ta yi horon ne da karfe bakwai na dare.
‘Yan wasan Black Stars a karkashin shugabancin Andre Ayew sun yi karfafawa karshe ga marigayi tsohon dan wasan Ghana Chirstian Atsu.
Ga dukkan alamu, ana dada neman cinikin dan wasan Chelsea din nan dan asalin kasar Ghana, Abdul Baba Rahman, a yayin da ita kuma Chelsea ke cewa, idan ya na so, ana iya sayar da shi.
Yayin da Ghana ke harmar inganta bangaren shari'arta don ya dace da zamani ya kuma dada tabbatar da adalci, Amurka ta ce za ta taimaka ma ta wajen cimma wannan burin.
A ci gaba da kokarin da wasu kasashen Afurka ke yi na dogaro da kai, kasar Ghana ta dukufa wajen kirkiro akasarin magungunanta a cikin gida. Wannan zai magance matsalar da ke tattare da dogaro da waje, sannan zai samar da ayyukan yi.
Bayan Isar Alhaji Aliyu Mustafa Sokoto, shugaban Sashen Hausa na Murya Amurka zuwa Accra, ya fara da ziyarar tashar talabijin mai suna Hijra TV a ranar Asabar, inda ya samu gagarumin tarbo daga shugaban tashar, Abdul Razak Toure da ma aikatan tashar.
Ziyarar Firai Ministar Denmark Mette Frederiksen ita ce ta farko a Ghana. Wannan ziyarar ta karrama cika shekaru sittin da huldar diflomasiya tsakanin Denmark da Ghana ce. ‘Yan kasar Denmark na ganin kasar Ghana a matsayin muhimmiyar kawar kawance a Afrika ta yamma da baki dayan Afrika.
Bayanai daga kungiyar likitocin Ghana sun tabbatar cewa, da kasar ta fada cikin barkewar annobar COVID-19 karo na uku kana binciken ya tabbatar da nau’in cutar ta Delta na barna a kasar.
Kulob kulob din kwallon kafa da ke kasar Ghana sun fara fafatawa a zagayen farko na shiga gasar zakarun Afirka.
Ya zuwa ranar 7 ga watan Maris mutane sama da dubu dari biyu da 250 ne suka karbi rigakafin COVID-19 a Ghana. Yankin Accra ne keda kaso mai yawa na wadanda suka karbi rigakafin, inda mutane 128,086 suka samu maganin kana yankin Ashanti ke bi ma shi da mutane 59,325 da suka karbi rigakafin.
Bayan danbarwar siyasa tare da wasu matsalolin zabe, a karshe an rantsar da Shugaban Ghana, Nana Akufo Addo na jam'iyyar NPP. Sai dai 'yan jam'iyyar NDC sun kaurace.
Yayin da kasar Ghana ke shirin gudanar da zabe a ranar Litinin mai zuwa, tawagar da za ta sa ido ta kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS ta isa kasar.
A cigaba da tabo wasu batutuwan tuna baya game da rayuwar marigayi tsohon Shugaban Ghana, JJ Rawlings, an dan tabo wasu halayyansa da su ka yi matukar banbanta shi da sauran shugabanni da kuma takaitaccen tarihinsa.
Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo ya gabatar da takardunsa na shiga takara a zaben shugaban kasa na ranar bakwai ga watan Disamba shekarar 2020 a kan tikitin jami’iyarsa ta New Patriotic Party ko NPP a takaice.
Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo kuma shugaban kungiyar kasashen raya tattalin arziki ta Afrika ta yamma, ECOWAS, ya yi kira ga takwarorin sa shugabannin Afrika ta Yamma da su yi kokarin kawo karshen rikicin kasar Mali.
Gwamnatin Kasar Ghana ta gabatar da kasafin kudi na rabin shekara wanda yake tafe da matakan sassauci ga 'yan kasa sanadiyyar bullar cutar coronavirus.
A yayin da ya ke yi wa al'ummar kasar jawabin shekara-shekara, Nana Akufo Addo, ya zayyana irin nasarorin da ya ce gwamnatinsa ta cimma a wannan wa'adin mulkin nasa. Ya kuma tabo mahimman batutuwa da kasar ke fama da su, ciki har da batun dawo da daliban Ghana daga China.
Domin Kari