Nana Akufo-Addo shine dan takara na farko da ya kai taradunsa ga hukumar zaben Ghana domin ya tabbatar ya shirya fafatawa da sauran ‘yan takara a zaben na Disamba. Shugaban ya je hukumar zaben ne tare da mataimakinsa Dr. Mahumud Bawumia wanda zai dafa masa baya a zaben mai zuwa.
Shugaba Akufo-Addo mai shekaru 76 a duniya da yake neman karin shekaru hudu ne a wa’adin mulkinsa na biyu, shine mutum daya tilo da ya gabatar da kansa yayin da jami’iyarsa ta bude ta kuma kulle amsar takardun masu neman yi mata takara a farkon wannan shekara.
Akufo-Addo zai fafata da tsohon shugaban kasa dan takarar babbar jami’iyar adawa ta National Democratic Congress ko NDC a takaice, John Dramni Mahama, wanda shima ya yiwa jami’iyarsa takara sau uku a jere. Mahama ya yita dora ayar tambaya a kan ayyukan hukumar zaben cewa ba zata gudanar da zabe mai inganci ba.
Shiko shugaban kasa Nana Akufo-Addo ya yabawa ayyukan da hukumar zabe take yi, yana mai cewa hukumar ta bashi da yawancin mutanen Ghana kwarin gwiwar cewa zata yi jagoranci da kwarewa kana zata shirya zabe na gaskiya da adalci kuma komai bayyane.
Yayin da ya gabatar da takardunsa ga hukumar zabe a jiya Talata, Akufo-Addo ya ce ‘yan Ghana suka sabonta wa’adin mulkinsa, kada ya zama a cikin zabe mai cike da magudi amma ya samu amincewar al’ummar kasar a kan zabe na gaskiya kuma a bar kowa ya zabi abin da yake so.
Shugaban hukumar zabe Jean Adukwei Mensa, ta ce hukumarta ta himmantu wurin shirya zaben gaskiya kamar yadda aka shirya a baya. Ta kuma ce hukumar ta tabbatar da wasu matakai na gudanar da bincike a kan masu takara kuma hakan ne yasa hukumar ta ba ‘yan takarar kwanaki biyar su gyara duk wasu kura kurai dake cikin takardunsu.
Ga rahoton Ridwan Abbas daga Accra:
Facebook Forum