Ma'abota Sashen Hausa sun bayyana ci gaban da aka samu da ke ba kowa damar sauraron radiyo, da suka hada da amfani da yanar gizo da kuma wayoyin hannu da aka fi sani da salula.
Tuni Wasu Kasashe Suka Fara Kwashe 'Yan Kasar Su Daga Birnin Wuhan Dake China Kuma Tushen Cutar CORONAVIRUS Wacce Humkumar Lafiya Ta Duniya WHO Ta Ayyana Dokar Ta Baci Akanta.
Hukumomi a kasar Ghana sun kara kaimi a yaki da cutar cizon sauro ko Maleriya, inda shirin yaki da cutar ke cigaba da samun tallafi da kuma kwarin gwiwar aiwatar da tsare tsare domin ganin an rage illar da cutar ke yiwa al’umma musamman kananan yara da mata masu juna biyu.
Alkaluma daga kungiyar sufurin sama ta kasa da kasa IATA a takaice sun nuna cewar Afrika ce ta ke samun bunkasa a fannin sufurin jiragen sama cikin gaggawa a shekaru ishirin masu zuwa kasancewar bukatar sufurin jiragen saman zai ninka.
Hukumomi a Ghana sun bayyana fargabar samun hare haren ‘yan ta’adda a cikin wannan lokaci, lamarin da yasa hukumomin tsaron kasar suka fara daukar matakan sa ido a kan harkokin jama’a tare da yin gargadi ga jama’a su kula kuma su taimakawa jami’ai da bayanai.
A cigaba da nuna misalin muhimmancin hakuri da juna, da hadin kai, da zama tare wanda magabata ke nunawa a lokacin watan Ramadan, Shugaban kasar Ghana da Mataimakinsa da sauran magabata sun yi bude baki da sauran jama'a.
Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, sun harbe suka kashe wani dan jaridar Ghana da ya kware a buga labaran da suka shafi abin fallasa kuma ma’aikacin kamfanin jarida na Tiger Eye PI mai suna Ahmed Hussein Suala, a unguwar Madina dake birnin Accra.
Da sanyin safiyan Litini aka soma wani atisayin rusa daruruwan gine gine dake kurkusa da layin dogon Accra zuwa Tema domin kare layin dogon daga hadura
Kasar Ghana tana ci gaba da fuskantar barazana a baya bayan nan sakamakon tashe tashen hankali da ake fuskanta a kasashe dake makwabtaka da ita.
Yau Talata shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo tare da wasu tawaga ta mussamam , ya karbi gawar marigayi Kofi Anan in da aka saukar da tutocin Majalisar Dinkin Duniya da ta Ghana kasa kasa, alamar cewa an mikawa Ghana gawar.
Kimanin shekaru 61 da suka gabata ne kasar Ghana ta samu 'yancin kai daga turawan Ingila da suka yiwa kasar mulkin mallaka kuma mutane irin su Dr. Kwame Nkurma shugaban kasar na farko da Dr. Danquah da sauransu suka yi gwagwarmayar kwatowa kasarsu 'yancin.