Shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo, ya sha alwashin fara biyan mutanen da kudadensu su ya makale a bankunan da suka durkushe daga ranar Litinin din nan mai zuwa.
Haka nan, ya lashi takobin hukunta duk wanda aka kama da hannu cikin durkushewar bankunan wanda yanzu ya zama wajibi akan gwamnatinsa ta biya mutanen da su ka yi ajiya a bankunan biliyoyin kudade, wanda ba don wannan ba, gwamnati zata yi amfani da su wajen gudanar da ayyukan raya kasa.
Sugaban kasar, ya ci gaba da bayyana irin nasarorin da gwamnatinsa ta cimma cikin wa’adin mulkinsa na farko, kana, ya ga fa’idar al’ummar kasar su sake zabansa a karo na biyu domin ya ci gaba da ayyukan gina kasa da ya fara. Sai dai kuma, wdannan kalaman, ba su faranta wa ‘yan adawa rai ba, abin da ya sanya su fice daga dakin taron kafin shugaban ya kammala jawabinsa.
Domin Karin bayani, a saurari cikakken rahoton Ridwan Mukhtar Abbas:
Facebook Forum