Ministan Kudin Ghana, Ken Ofori Attah, wanda ya gabatar da Kasafin Kudin a gaban Majalisar Dokokin Kasar, ya bayana cewa abubuwa sun yi tsauri tun daga lokacin da gwamnatinsu ta karbi Mulki a shekarar 2017. Saboda haka, inji shi, gwamnati ta yi kokari wajen ganin al'amura sun yi sauki.
Ministan ya ce, fannin noma ya samu gagarumin cigaba a wannan lokaci, inda gwamnatin Akufo Addo ta zuba jarin Cidi Biliyan 1.8 a fannin aikin gona.
Yace, gwamnatin ta kuma kafa masana’antu saba’in acikin shirin gunduma daya masana'anta daya, wanda a yanzu haka suna aiki gadan-gadan.
Ya kara da cewa gwamnati na taka tsantsan wajen kashe kudi yadda ba zai haura gibin kasafin kudin ba. Ya ce saboda da matsalar tattalin arziki da cutar corona ta haifar ma jama'a, gwamnati ta dau wasu matakai na sassauta kuncin rayuwa.
A saurari cikakken rahotan Ridwan Abbas:
Facebook Forum