NAHCON ta ce duk kamfani sai ya gabatar da shaidar mallakar Naira miliyan 30 a ajiye a banki da kuma ba da ajiyar Naira miliyan 25 don kare muradun alhazai idan an saba musu ka'ida.
A jawabin shi sabon jami'in yada labarai na kungiyar dattawan ta arewa da farfesa Ango Abdullahi ke jagoran ta, Malam Abdul'aziz Sulaiman, ya ce ya zama wajibi 'yan arewa su hada kai wajen kawar da bambance-bambance da fuskantar abubuwan da za su dawo da zaman tare a yankin.
Sabon shirin AREWA A YAU zai tabo alwashin mai taimaka wa shugaba Tinubu kan lamuran nakasassu Komred Muhammad Abba Isa, na janye masu bara daga kan tituna da ma dawo da masu nakasa na arewa da su ka shige jihohin kudancin Najeriya.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya aikawa majalisar dokokin Najeriya takardar neman amincewarta domin ciwo bashin zunzurutun kudi dala biliyan 8.69 da kuma Fam miliyan 100.
Kasafin ya amince da sanya canjin dala a kan Naira 700 sai kuma gangar man fetur a kan dala 73.96.
Sai dai fadar shugaban kasar ta Najeriya ta ce Babachir yana wadannan kalaman ne saboda har yanzu yana fama da takaicin nasarar da Tinubu ya samu a zaben da aka yi.
Hukumar alhazan Najeriya NAHCON ta nanata umurnin ajiye Naira miliyan 4.5 daga duk mai niyyar gudanar da aikin Hajjin 2024 gabanin karshen watan gobe.
Wasu lauyoyi masu da'awar kishin al'ummar Nijar sun shigar da kara kotun ECOWAS a Abuja don bukatar haramta takunkumi kan talakawan Nijar.
Yayin da ma'aunin tashin farashin kayan masarufi ya kai kashi 27.33% bisa rahoton hukumar kididdiga ta Najeriya, masana sun ba da shawarar komawa kan kananan sana'o'i don samun mafita.
Hadaddiyar kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC da TUC ta ayyana tsunduma gagarumin yajin aiki daga ranar Talatar nan ne har sai baba ta gani.
Hukumar raya Babban Birnin Tarayya na Abuja ta ce sam ba kamshin gaskiya a labarin da aka yi ta yayata a kafafen sada zumunta cewa Ministan birnin Nyesom Wike zai rushe wani sashen babban Masallacin tarayya da ke Abuja.
Jakadan Falasdinu a Najeriya, Abdullah Shawesh, ya ce cikin wadanda ke gwagwarmayar kwato wa Falasdinawa hakkinsu akwai mabiya addinin kirista da ma Yahudawa.
Domin Kari