Sabon shirin AREWA A YAU zai duba muhimmancin kafa gidauniya don raya lamuran ilimi a yankin arewacin Najeriya.
Hakika akwai miliyoyin yara da ke kan titunan arewa ba tare da samun damar shiga makaranta ko samun ilimin addini da ma na zamani ba.
Wasu jihohin kan kafa gidanuniya don taimaka wa raya ilimi ta hanyar gyara makarantu, sayan kayan aiki da sauran su don tallafa wa makarantun gwamnati su iya gogayya daidai gwargwado da makarantu masu zaman kansu.
Kwarerrre kan ilimi Dr. Kole Shettima ya duba muhimmancin matakin kafa gidauniya da yanda yara da dama ke zama ba tare da samun ilimi ba.
Yanzu za mu leka jihar Yobe da ke cikin jihohin da ke farfadowa daga illar Boko Haram wadda kuma ta kafa gidanuniya don tallafa wa neman ilimi.
Bayan rangadi na ayyukan gidauniyar shugaban ta, Injiniya Muhammad Abubakar, ya bayyana abubuwan da ya ce sun tabuka.
Saurari shirin:
Dandalin Mu Tattauna