Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Zai Gabatar Da Kasafin Kudin 2024 Ranar Laraba


Shugaba Tinubu (Hoto: Facebook/Bola Tinubu)
Shugaba Tinubu (Hoto: Facebook/Bola Tinubu)

Kasafin ya amince da sanya canjin dala a kan Naira 700 sai kuma gangar man fetur a kan dala 73.96.

Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta amince da kasafin kudin badi (2024) a matsayin Naira tiriliyan 27.5.

Hakan ya zama kari a kan hasashen farko na kasafin da Naira tiriliyan 1.5.

Ministan kasafin kudi Atiku Bagudu ne ya bayyana hakan bayan Taron Majalisa Zartarwa da Shugaba Tinubu ya jagoranta a ranar Litinin.

Kasafin ya amince da sanya canjin dala a kan Naira 700 haka nan ita kuma gangar man fetur a kan dala 73.96.

Yanzu dai har gwamnatin na shirin mika kasafin ga majalisar dokokin tarayya don amincewa.

Fadar shugaban kasar ta ce a ranar Laraba Tinubu zai gabatar da kasafin kudin ga gamayyar Majalisar Dokokin kasar.

A zamanin gwamnatin Buhari, kasafin kudin Najeriya ya dawo aiki daga watan Janairu zuwa Disamba.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG