ECOWAS dai ta aza takunkumi kan Nijar biyo bayan juyin mulkin sojoji da su ka kifar da gwamnatin Muhammad Bazoum.
Lauyoyin, wadanda ba su amince gwamnatin sojan Nijar ta Janar Abdulrahman Tciani ce ta turo su ba, sun ce sam ba daidai ba ne in a na tuhumar sojoji da laifi, a hada har da al'ummar Nijar.
Metri Ahmed Mammane na wakiktar wasu mutum 7 masu son a janye takunkumi kan Nijar ya ce ya na da kyau a duba kadun fararen hula na Nijar da rufe kan iyaka ya jefa rayuwar su a garari.
Shi ma lauya Metri Isma’il Tambo Mousa ya ce al'ummar Nijar na mawuyacin yanayi don haka kotun ta tilastawa ECOWAS ta janye takunkumin in ya so ta san hanyar da za ta dau mataki kan masu juyin mulki.
Kotun ta dage zama kan batun zuwa 7 ga watan gobe don yanke hukunci.
Jami'an tsohuwar gwamnatin Nijar irin su Dokta Manzo Abubakar sun sha nanata bukatar dawo da ragama hannun farar hula ko ma shugaba Bazoum don samun sulhu mai dorewa.
Da alamu ECOWAS da ke zaman babbar kungiyar tattalin arzikin Afirka ta yamma na son amfani da takunkumin wajen horar da sojojin juyin mulki a madadin matakan soja da ke samun suka daga bangarori da dama.
Saurari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna