Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Don Karbo Bashin Dala Biliyan 8.69 da Fam Miliyan 100


Shugaba Bola Ahmed Tinubu (Facebook/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu)
Shugaba Bola Ahmed Tinubu (Facebook/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu)

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya aikawa majalisar dokokin Najeriya takardar neman amincewarta domin ciwo bashin zunzurutun kudi dala biliyan 8.69 da kuma Fam miliyan 100.

Shugaban ya ce za’a yi amfani da lamunin ne wajen gudanar da wasu muhimman ayuka da suka hada da wutar lantarki da hanyoyi da ruwan sha da hanyoyin jiragen kasa da kuma kiwon lafiya.

Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio da Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas sun gabatar da wasikar ta shugaban kasa ga 'yan majalisar.

Wannan neman lamunin dai kari ne kan neman hurumin karbo lamuni da Tinubu ya yi a baya da majalisar ba ta kai ga amincewa da shi ba.

Wasikar da Tinubu ya aika a baya, ta kunshi neman lamunin dala biliyan 7.86 da kuma Fam miliyan 100.

Takardar ta nuna wannan na daga cikin tsarin cin bashi na shekara ta 2024 mai shigowa.

Fadar shugaban kasar ta ce a ranar Laraba Tinubu zai gabatar da kasafin kudin ga Majalisar Dokokin kasar.

A zamanin gwamnatin Buhari, kasafin kudin Najeriya ya dawo aiki daga watan Janairu zuwa Disamba.

An tabbatar gwamnatin tsohon shugaba Muhammadu Buhari da ta gabata ita tafi kowace gwamnati a tarihi kasar cin bashi, da hakan ya nuna yanzu za'a jira a ga zuwa karshen mulkin Tinubu ko zai iya tsallake mizanin ko kuwa a'a.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG