A cikin shirin na wannan makon, mun duba muhimmancin kafa tasoshn sauke hajar teku a tudu a yankin Arewacin Najeriya da ba ya kusa da gabar teku.
Karin kwana goma da babban bankin Najeriya ya yi don canja tsoffin kudi ya rage zullumin jama'a da ke fafutukar yin canjin.
Dan takarar Shugaban kasa na NNPP, Rabi'u Kwankwaso, ya ce ba wanda zai yi asarar kudin sa matukar ya hau karagar mulki.
A cikin shirin na wannan makon, bangare ne na karshe da ya duba yadda tarihin yankin Arewa ya ke a baya inda mutane kan taimakawa juna ta hanyar marabtar baki, kyautata makwabta, tallafawa marayu da sauran su.
Masana na baiyana cewa sai ‘yan Najeriya a dukkan sassa sun yi zabe nagari ba da la’akari da wani bambanci ba ne za a iya samun cin gajiyar arzikin kasar mai yawa.
Najeriya ta samu nasarar yin taro da hukumomin aikin hajji na Saudiyya, inda aka sanya hannu kan yarjejeniyar gudanar da aikin hajjin bana.
Hukumar zaben Najeriya ta INEC ta bayyana cewa, ba a fahimci kalaman jami’inta mai kula da cibiyar horarwa kan zabe bane, wato Farfesa Abdullahi Zuru, akan fargabar da ake fuskanta game da zaben.
A cikin shirin na wannan makon mun ci gaba ne da wanda mu ka fara a makon jiya da ya duba yadda tarihin yankin Arewa ya ke a baya inda mutane kan taimakawa juna ta hanyar marabtar baki, kyautata makwabtaka, tallafawa marayu da sauran su.
Babban bankin Najeriya CBN na kan bakan sa na dakatar da aiki da tsoffin kudi a karshen watan nan duk da bukatar tsawaita lokacin daga majalisar dattawa.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar an gudanar da zaben 2023 cikin adalci inda za a damka ragama ga wanda mutane su ka zaba.
A cikin shirin na wannan makon mun duba yadda tarihin yankin Arewa ya ke a baya, inda mutane kan taimakawa juna ta hanyar karbar baki, kyautata wa makwabta, tallafawa marayu da sauran su.
Dan takarar jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya musanta labarin da ke cewa ya gana da wasu gwamnoni su 5 da su ka yi wa PDP a London.
Masu sha'awar kwallon kafa da ma sauran jama'a a fadin duniya na ci gaba da nuna alhini kan rasuwar shahararren dan wasan kwallon kafan nan na kasar Brazil , Pele.
A cikin shirin na wannan makon bita ce ta karshe ta shirin a shekara ta 2022 mai bankwan, mun duba koyar da matan Fulani makiyaya da ke zama a dazuka sana'o'i don samun dogaro da kai ko da wani dalili zai sa su rasa shanun su.
Domin Kari