Wannan bayanin dai na kunshe ne a wata sanarwa daga mai magana da yawun dan takarar APC wato Tunde Rahman, wanda ya ce wasu ne kawai suka kirkiro labarin don cimma muradinsu na siyasa.
Ko da yake, Rahman ya kara da cewa Tinubu na da ‘yancin ganawa da duk wani gwamna ko kungiyar da ya yi muradi don bunkasa siyasarsa.
Rahotanni sun bayyana cewa shi kansa madugun gwamnonin 5 wato gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike, ya musanta labarin cewa sun gana da Tinubu a lokacin da ya dawo Najeriya daga London.
Dan kwamitin gudanarwa na APC Dattuwa Ali Kumo, wanda shi ma ya na London a lokacin, ya ce in Allah ya yarda nan ba da dadewa ba wadannan mutanen da ma wasu kusoshin jam'iyyar PDP zasu fito su bayyana goyon bayansu ga dan takararsu na jam'iyyar APC.
Jigajigan jam'iyyar PDP irinsu tsohon gwamnan jihar Sokoto Attahiru Bafarawa, na cewa aikin baban giwa ne ga gwamnonin tun da suna takarar mukamai a inuwar jam’iyyar ta PDP.
Ko dai gwamnonin sun gana ko ba su gana da Tinubu ba, gwamnonin sun nuna bara'arsu ga dan takarar jam’iyyarsu Atiku Abubakar.
Alamu na nuna PDP na shirin sa kafar wando daya da gwamnonin da ke ci gaba da daukar matakan angulu da kan zabo ga jam’iyyar.
Saurari rahoton cikin sauti: