Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN 2023: Masu Zagon Kasa a Aso Rock Ba Su Da Goyon Bayan Shugaba Buhari - APC


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Yake Magana Yayin Kaddamar Da Sabbin Naira
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Yake Magana Yayin Kaddamar Da Sabbin Naira

APC na magana ne kan zargin da gwamnan Kaduna Nasir Elrufai ya yi cewa akwai mukarraban shugaba Buhari da ke angulu da kan zabo ga jam'iyyar.

Dan kwamitin gudanarwa na jam'iyyar, Dattuwa Ali Kumo, ya ce su na da tabbacin Shugaba Buhari na mara baya 100 bisa 100 ga Tinubu kuma zai ma bayyana a wasu jihohi don taya Tinubun yakin neman zabe.

Dattuwa Kumo ya bugi kirjin cewa PDP da a ke raderadin wasu manyan APC na marawa baya ba za ta kai labari ba a zaben.

Dan Kwamitin Gudanarwa Na Jam'iyyar APC, Dattuwa Ali Kumo
Dan Kwamitin Gudanarwa Na Jam'iyyar APC, Dattuwa Ali Kumo

Shi ma mamba a ofishin kamfen din APC Barayan Bauchi, Sunusi Baban Takko, ya ce hatta ficewar Hajiya Naja'atu daga kamfen din zuwa marawa Atiku na PDP baya bai tayar mu su hankali ba don shi da wasu dattawan arewa ne mafi yawan kuri'a su ka fara ayyana goyon baya ga Tinubu.

Da ya ke martani kan dambarwar mataimakin shugaban PDP, Umar Iliya Damagum, ya ce ba wanda ya fi dan takarar su Atiku tagomashin lashe zaben.

Mataimakin Shugaban Jam'iyyar PDP, Umar Iliya Damagum
Mataimakin Shugaban Jam'iyyar PDP, Umar Iliya Damagum

Yayin da a ke saura mako 3 a gudanar da zaben, ba yanayin marmarin tinkarar zaben musamman a Abuja, don mutane sun fi maida hankali ga neman kudi a na'urar ATM.

Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-hikaya:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG