Wannan na zuwa ne daidai da takaita fitar da kudi a wuni.
Gwamnan babban bankin Godwin Emefiele ya baiyana cewa tsoffin kudin za su cigaba da aiki zuwa 31 ga watan nan na Janairu amma daga nan sai sabbin kudin kadai.
Fargabar rashin wadatar sabbin kudin da zuwa yanzu alkaluman bankin na nuna an buga kimanin Naira miliyan 500 ne na karuwa kuma wa'adin dakatar da tsoffin kudin na karatowa.
Sanata Haruna Garba wanda masanin harkar kudi ne ya ce bin shawarar majalisa da tura daina canjin zuwa watan Yuni ne mafi a'ala.
Dan majalisa Gudaji Kazaure da ke cigaba da aikin binciken cajin shigarwa da fitar da kudi a banki, ya ce illar da canjin zai kawo ba zai misaltu ba.
Wasu bankuna sun tura sako cewa za a iya samun sabbin kudin a na'urorin ATM a fadin kasar da fitar da Naira dubu 100 ga daidaiku kana dubu 500 ga kamfanoni.
Saurari rahoton a sauti: