ABUJA, NIGERIA - Shugaban ya bayyana haka ne a sanarwar sabuwar shekarar nan ta 2023 da a ka shiga a farkon makon nan.
Bayanin ya tabo lamuran kasa da dama kuma shugaban na nuna shekarar ta 2023 na da muhimmanci gare shi da kuma sauran ‘yan Najeriya saboda kokarin da za a yi na zabe da za a samu sake mika mulki ga wata sabuwar gwamnatin farar hula.
Alwashin shugaba Buhari har kullum shi ne zai damka gwamnatin hannun duk wanda ya lashe ko kuma a ce ga duk wanda ‘yan Najeriya su ka zaba.
Ga lamuran tsaro shugaban ya yaba wa dakarun tsaro saboda himmar da su ke yi inda ya ce za a kara ba su kwarin gwiwar aiki don dawo da zaman lafiya mai dorewa.
Masanin kimiyyar siyasa na jami’ar Abuja, Dr. Farouk B. B. Farouk, ya ce yanda kamfen ke gudana na nuna za a iya samun wani sauyi da ba a taba samu a zabukan da aka gudanar a baya ba.
Jami’a a sashen labaru ta hukumar zabe, Zainab Aminu, ta nanata cewa hukumar za ta yi amfani da na’urar tantancewa ta BVAS da za ta hana duk wani yunkurin magudi.
Za a gudanar da babban zaben a ranar 25 ga watan gobe da kuma ranar 11 ga watan Maris na shekarar nan.
Kamfen na ci gaba da gudana tun fara shi a shekarar da ta gabata.
Saurari cikakken rahoto daga Nasiru Adamu El-hikaya: