Makwanni biyu bayan cire tallafin man fetur, manoma na ci gaba da jan hankali kan yadda suke so sabuwar Gwamnati a karkashin Shugaban Kasa Ahmed Bola Tinubu ta yi amfani da rarar kudin tallafin wajen habbaka harkar noma a kasar, amma kwararru na ganin ba abu ne da zai yiwu a kankanin lokaci ba.
A yau talata ne, Majalisar Dattawan Najeriya ta zabi tsohon Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio, a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa ta 10. Duk da adawa da aka yi ta nunawa a lokacin da ake ta Kamfe akan kujerar , Jam'iyyar APC ta ce Akpabio ta fi so da mukamin.
Wasu kungiyoyi Masu rajin kare kabilar Igbo daga Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas sun ce tube Gwamnan Babban Bankin Najeriya tare da tsare shi da hukumomin tsaro suka yi, na nuna cewa Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta fara wariyar jinsi a kan kabilar Igbo.
Wannan kudurin dokar ya bayyana yadda tsarin fansho na 'yan sandan Najeriya ya ke fama a karkashin tsarin bayar da gudummuwar fansho ta kasa, wato PENCOM
Wasu kungiyoyin manoma a Najeriya da dama sun ce suna goyon bayan cire tallafi man fetur da gwamnati ta yi, amma sun bukaci a habaka harkar noma a kasar.
Tsofaffin Sanatoci da ke karkashin inuwar Jamiyyar APC mai mulki a Najeriya sun yi gagarumin taron inda suka kafa kwamiti na musamman da zai yi tuntuba a gabanin zaben sabbin shugabanni a Majalisar dokokin kasar.
Tinubu ya bayyana haka a jawabin sa na farko da ya yi bayan rantsar da shi a matsayin shugaban kasa. Sai dai wasu sabbin ‘yan majalisa sun bayyana ra'ayoyi mabanbanta kan batun yin aiki tare da bangaren gwamnati.
Majalisar dokokin Najeriya ta amince da dokar da za ta ba yan kasa damar tsayawa takara na kashin kai. Tuni an mika dokar ga shugaban kasa domin ya rattaba mata hannu ta zama doka.
Kuma tuni an mika dokar ga shugaban kasa domin ya rattaba mata hannu ta zama doka. Daga dukan alamu dokar ta samu karbuwa domin ‘yan majalisar sun ce dokar ba ta su ba ce.
Bincike ya yi nuni da cewa mata kan cika rumfunan zabe da dama a sassan Najeriya a duk lokacin da ake zabe.
An samu mahalarta taron daga kasashen duniya daban daban ciki har da Amurka. Taron zai duba abubuwa da dama kama daga gudunmawar da kafafen yada labarai su ke bayarwa wajen inganta cinakayya da kalubalen yada shirye shirye a yanayi na na'ura mai aiki da kwakwalwa da kuma dijital ko lataroni.
Tsofaffin Sanatoci 77 na Jamiyyar APC gami da sabbi masu yawa ne suka sha alwashin yin tuntuba tare da hada kai da masu ruwa da tsaki, domin tabbatar da nasarar Sanata Godswill Akpabio da Barau Jibrin a matsayin shugabannin Majalisar a karo na 10, kamar yadda uwar jam'iyya ta nema.
Rahoton da Ofishin kula da basussuka ya fitar na kwata na hudu na shekarar 2022 ya nuna cewa jimlar bashin da ake bin Najeriya a wannan lokacin ya haura Naira Triliyan 46.25
A daidai lokacin da ake samun kiraye-kiraye daga Kungiyoyi daban-daban kan shugabancin Majalisar Dokokin Najeriya, a ranar Litinin jam’iyyar APC ta sanar da shiyyoyin da shugabannin Majalisar za su fito.
Akwai Madam Hassana Ayuba Mairiga Tula wacce lauya ce tare da 'yar gwagwarmayar kwato wa mata yanci Hajiya Balaraba Abdullahi, su ma sun yi nazari a wannan shirin.
Ma'aikatar Jinkai da Walwalar Jama'a ta Najeriya, ta yi karin haske kan dalar Amurka Miliyan 1.2 da aka kashe, kan batun samun motocin sufuri don kwashe 'yan Najeriya wadanda yawancin su dalibai ne zuwa gida daga Sudan da ke fama da yaki.
Bankin Duniya ya ce Najeriya na cikin wani yanayi mai rauni tun shekaru biyu da suka wuce, lokacin da aka samu tashin farashin mai a karshen shekara 2021.
Matan sun bayyana tarihin siyasarsu da yawan shekaru da suka kwashe suna gwagwarmaya a wannan fagge da maza suka fi yawa.
Yan Jamiyyar APC mai mulki, da suka hada da shugabani, da Gwamnoni, da jiga jigan jamiyyar, na ta takun saka a kan batun raba manyan mukamai a Majalisar Dokokin Kasa ta 10 mai zuwa, inda batun addini ke neman taka muhimmiyar rawa.
Domin Kari