ABUJA, NIGERIA - Masu fashin baki a al'amuran yau da kullum na ganin an yi hanzari wajen cire tallafin na man fetur da ya kasance wani abin alhaki ga kasafin kudin Najeriya har kwararru suka ce tallafin yana gurbata kasuwanni da hana saka hannun jari.
Wasu kuma sun yi ikirarin cewa akwai tallafi inda gwamnati ta kasa aiwatar da shirye-shirye don shigar da farashi mara kima.
Kungiyar matasa manoma ta Najeriya a ta bakin shugaban su Dr. Abubakar Bamai Musa ya ce kungiyar tana goyon bayan cire tallafi da gwamnati ta yi.
Bamai ya ce cire tallafin yana kan gaba domin idan aka lura da makudan kudaden da ake kashe wa a kullum za a ga cewa al'umma ba sa more komi a tallafin da gwamnati ta ke kashewa.
Bamai ya ce matasa sun fi kowa yawa a kasa kuma su ne ba su da ayyukan yi, saboda haka suke kira ga gwamnati da ta zuba kudaden wajen inganta noma saboda matasa su samu aikin yi.
Bamai ya kara da cewa sun riga sun tantance matasa da ke da sha'awar noma, saboda haka a shirye su ke su hada kai da gwamnati wajen gano matasan domin a ba su tallafin noma da kuma kama noman dabbobi, da kifi da kayan abinci saboda dogaro dakai.
Bamai ya ce akwai hekta miliyan 80 da ba a nome ba a kasar kuma ana da matasa miliyan kusan 70, idan an ba kowane matashi hekta daya, kasa za ta wadatu da abinci har a sayar wa kasashen waje.
Shi kuwa shugaban kungiyar manoman dabbobi Samaila Bulama, ya koka cewa da gwamnatin da ta shude an ware su wajen samun tallafin noma saboda haka suke kira da babban murya a yanzu ganin cewa sabon gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ce za ta karfafa noma ta bangarori daban daban saboda kasa ta wadatu da nama har ta ciyar da kanta da kayan da ta noma ko da ba a rufe boda ba.
Samaila ya ce suna kira da babban murya cewa gwamnati ta tuna da su a wannan karon don a basu tallafi saboda aikin kiwo da noma su tafi daidai a bisa tsari na hadin kai domin inganta zaman lafiya.
Ita kuwa shugabar kungiyar mata manoma ta Najeriya Amina Kabir Mala ta yi tsokaci cewa mata ne kan gaba a harkar noma a kasar inda ta bada hujja cewa su ne suke daukan nauyin iyalan su yanzu fiye da maza, saboda haka suke kira ga gwamnati da ta tabbatar ta ba su tallafi mai tsoka daga ciin kudin tallafin da za a tara a yanzu.
Amina ta ce mata sun fi kowa biyan bashi in an ba su. Amma ga tsohon shugaban kungiyar ma'aikatan man fetur ta kasa Komred Isa Tijjani ya ce ba za su yarda da wannan cire tallafi da akayi ba.
Tijjani ya ce ba zai yiwu ba, saboda tallafi ba karin kudin mai ba ne kawai, akwai fannoni da yawa da ya kamata a duba kafin a cire tallafi.
Tijjani ya ce a yi setin kasa ta yanda mutane za su samu saukin rayuwa kafin a yi maganan cire tallafi.
Kungiyoyi kwadago irin su NLC da TUC suna ta gana wa da bangaren gwamnati kan batun cire tallafin, inda suka ce zasu fito da mataki gobe Litinin kan shiga yajin aikin gama gari a ranan Laraba ko akasin haka.