Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawan Najeriya Ta Amince Da Kudirin Kafa Hukumar Fansho Ta 'Yan Sanda


Hukumar Kula Da Ayyukan ‘Yan Sandan Najeriya
Hukumar Kula Da Ayyukan ‘Yan Sandan Najeriya

Wannan kudurin dokar ya bayyana yadda tsarin fansho na 'yan sandan Najeriya ya ke fama a karkashin tsarin bayar da gudummuwar fansho ta kasa, wato PENCOM

A daidai lokacin da majalisar dattawan Najeriya ke haramar kammala aikin ta, sai gashi ta amince da wata muhimmiyar doka da za ta yi kokarin sauya rayuwar tsofaffin 'yan sanda, domin kuwa majalisa ta amince da maida tsofaffin 'yan sandan a karkashin hukumar fansho ta 'yan sanda maimakon hukumar fansho ta kasa ta PENCOM.

Wannan kudurin dokar ya bayyana yadda tsarin fansho na 'yan sandan Najeriya ya ke fama a karkashin tsarin bayar da gudummuwar fansho ta kasa ta PENCOM, wanda ya nuna cewa ana da bukatar kafa hukuma ta musamman ta 'yan sanda kamar yadda sauran hukumomin tsaro suke da ta su hukumar ta fansho.

Pencom
Pencom

Sanata Elisha Abbo, shi ne ya fara kawo kudurin neman a sauya wa 'yan sandan tsarin fansho a zauren majalisar dattawa.

"Idan aka duba batun fansho na 'yan sanda, sojojin kasa da na sama, da 'yan sandan farin kaya, da ma jami'an leken asiri, za a ga bambanci a tsarin fanshon da suke karba, abin da Abbo ya bayyana wa Muryar Amurka kenan.

Ya kara da cewa, mukamin kwamishinan 'yan sanda daya ne da na babban sakatare a ma'aikatar gwamnati, amma kudin fanshon sa a wata Naira 75 ne, idan aka kwatanta da sauran 'yan uwan sa na hukumomin tsaro da ke karbar Naira miliyan daya ko ma fiye, shi ya sa ya nemi a kafa hukumar fansho ta 'yan sanda domin a rika kula da su bayan sun ajiye aiki.

Wannan kudurin dokar dai ya samu karbuwa a majalisar dattawa duk da cewa an kwashi lokaci mai tsawo ana kai gwaro a kai marri akan sa, abin da Sanata Dauda Halliru Jika, shugaban kwamitin kula da harkokin 'yan sanda ya ce sun dauki dogon lokacin ne domin zurfafa bincike kan hukumomi irin na masu kayan sarki, da kuma tantance irin matsalolin da ka iya tasowa bayan an kafa hukumar.

Rundunar yan sanda
Rundunar yan sanda

Jika ya ce sun san irin matsalolin da tsofaffin 'yan sanda ke fuskanta, shi ya sa majalisar ta goyi bayan kudurin dari bisa dari. Ya kara da cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ma zai sa hannu a dokar domin ya san irin wahalar da 'yan sanda ke fuskanta bayan sun yi ritaya.

To ko yaya tsofaffin 'yan sanda suka ji da aka amince da dokar kafa masu hukumar fansho?

Abubakar Abdullahi Dashe, babban jami'i ne da ya ajiye aiki tun shekara 2008, ya bayyana farin cikinsa, inda ya ce ya dade yana karbar Naira dubu 30 bayan ya bar aiki yana da anini uku.

Dashe ya ce da shi da sauran 'yan sanda da ba su riga sun yi ritaya ba, yana murna a madadin su. Ya kuma yi wa majalisar dattawan addu'a da fatan Allah ya sa ta gama aiki lafiya.

Da ya ke jawabi bayan amincewa da dokar, shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan ya yaba da matakin majalisar, inda ya ce tabbatar da gaskiya da adalci wajen biyan fansho zai kara wa ma'aikatan 'yan sanda kwarin gwiwa, tare da inganta rayuwar wadanda suka yi ritaya.

Saurari rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG