Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawan Najeriya Ta Zabi Tsohon Gwamnan Jihar Akwa Ibom Godswill Akpabio A Matsayin Shugaban Majalisar Dattawa Ta 10


  Zababben Sabon Shugaban Majalisar dattawan Najeriya Godswill Akpabio da tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari
 Zababben Sabon Shugaban Majalisar dattawan Najeriya Godswill Akpabio da tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari

A yau talata ne, Majalisar Dattawan Najeriya ta zabi tsohon Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio, a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa ta 10. Duk da adawa da aka yi ta nunawa a lokacin da ake ta Kamfe akan kujerar , Jam'iyyar APC ta ce Akpabio ta fi so da mukamin.

Zababben Sabon Shugaban Majalisar dattawan Najeriya Godswill Akpabio ya yi rantsuwar kama aiki, bayan da Magatakardar Majalisar Sani Magaji Tambuwal ya aiyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri'u 63 inda abokin hamaiyyarsa kuma tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari ya tashi da kuri'u 46.

Tsohon Gwamnan Jihar Akwa Ibom Godswill Akpabio
Tsohon Gwamnan Jihar Akwa Ibom Godswill Akpabio

Sanata Mohammed Ali Ndume shi ne ya gabatar da Godswill Akpabio ga majalisar dattawan, ga abin da ya bayyana wa Muryar Amurka bayan an kammala zaben shugaban.

Ndume ya ce yana hamdala ga Allah ganin cewa an yi zabe lafiya kuma an gama lafiya tare da fatan zai cika wa al'ummar kasa burinsu kamar yadda Allah ya shirya.

Sanata Mohammed Ali Ndume
Sanata Mohammed Ali Ndume

Ndume ya ce shi ya fito ya zabi dan kudu domin a ga cewa Jam'iyyar APC mai mulki, jam'iyya ce mai adalci. Ndume ya ce yana ganin an zo gabar da za a yi mulki kamar yadda ya dace.

Shi ma daya daga cikin wadanda aka yi zaben shugabanin da su, Sanata Abdul Ningi daga Jihar Bauchi, ya yi tsokaci ne akan hujjojin da su ka shi ya zabi tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, a maimakon wanda aka zaba.

Ningi ya ce an fafata yadda dimokradiyya ta gindaya duk da cewa shi ba ya son salon mulkin APC amma ba shi da wani abu da zai yi, saboda haka Allah ya tsara abin shi, amma Ningi ya ce zai yi kokari ya sake renon Jam'iyyar PDP ta wajen yin kudurori da dokokin da za su ja hankalin yan kasa.

Rantsarwar Shugabanin Majalisar Dokokin Najeriya
Rantsarwar Shugabanin Majalisar Dokokin Najeriya

A bangaren Majalisar Wakilai kuma, Tajuddeen Abbas daga Zaria, Kaduna shi ne aka zaba da gagarumin rinjaye, inda ya samu kuri'u 353; sannan abokan hamayyarsa, Ahmed Wase da Aminu Jaji, kowannensu ya samu kuri'u 3 ne kacal, wani abu da ya sa dan Majalisa Hassan Shehu Hussein daga mazabar Nasarawa ta JIhar Kano ya ce yan majalisar sun yi zabe ne na cancanta.

Hassan ya ce sabon Kakakin Majalisar Wakilai Tajuddeen Abbas haziki ne, kuma dama kujerar ta masu rinjaye ce a Majalisar. Hassan ya ce abu ne mai wuya a samu dan adawa a irin wannan zubin. Hassan ya ce babu dan Majalisa wanda ya kawo dokoki masu yawa kamar shi sabon Kakakin. Saboda haka an zabe shi ne a bisa kwarewarsa da kuma cancantarsa.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya ci zabe ne ba tare da hamayya ba, haka shi ma mataimakin Kakakin Majalisar wakilai Benjamin Kalu .

Saurari rahoton :

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:23 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG