Wadannan kalaman na zuwa ne bayan da wani babban wakilin koriya ta kudu ya koma gida daga wata ziyara ta kwanaki biyu zuwa koriya ta arewa inda ya gana da shugaba Kim Jong Un.
A ci gaba da binciken zargin katsalandan din da Rasha ta yi a zaben Amurka na 2016, wata jami'a a gwamnatin shugaba Donald Trump, ta amsa tambayoyin kwamitin majalisar dokokin Amurka.
Cikin matsanancin fushi, masu zanga-zanga a Lardin Khyber Pakhtunkhwa da ke Pakistan suka kutsa ofisoshin kungiyoyin mayakan sa-kai da ake zargi da kisan dalibin wata jami’a daga yankin kudancin Waziristan.
Kasar Mozambique ta na musanta zargin da ake yi mata na cewa ta na ci gaba da huldar kasuwanci da Korea ta Arewa wanda hakan ya saba takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta saka wa Korea ta Arewan.
Wata kotu a birnin tarayyar Abuja ta Najeriya ta sake ingiza keyar matar nan Maryam da ake tuhuma da kashe mijinta Bilyaminu zuwa gidan kurkukun Suleja, bayan da mai shari'a yaki amincewa da bada belinta.
Taron shugabannin kasashen yankin Sahel, da na wasu kasashen Turai da kuma Asiya da ya gudana jiya Laraba a Faransa ya bada sanarwar samarda miliyan fiye da 100 na dalar Amurka a matsayin gudunmuwa don gudanar da ayyukan rundunar hadin guiwar G5 Sahel mai yaki da ta’addanci a yankin na Sahel.
Taron da aka gudanar na bana akan bunkasa amfani da iskar gas wajen girki a birnin Ikko, ya bayyana da cewa kashi biyar ne kacal daga cikin dari na al’ummar Najeriya ke amfani da iskar Gas a Najeriya wajen girki.
A makon da ya gabata ne gwamnan Neja ya ayyana wasu manyan biranen jihar a matsayin inda aka fi samun karancin abinci da kuma jama'a 'yan maula.
Kungiyoyi masu zaman kansu sun nuna bacin ransu akan wannan matakin da ake shirin dauka don gyara musu zaman, suna masu cewa ana so ne kawai a danne masu hakkokinsu na gudanar da ayyukansu a kasar.
Hukumar bada agajin jinkan Najeriya, ta fara kai agajin jinkai ga wadanda rikicin makiyaya da 'yan Bachama ya shafa a jihar Adamawa, Najeriya.
Fafaroma ya nuna rashin amincewarsa da shirin da shugaban Amurka Donald Trump keyi na amicewa da Qudus a zaman babban birnin Isra'ila, yayin da sauran kasashen duniya kamar Britaniya suka ce har yanzu Tel Aviv suka sani a zaman hedkwatar Isra'ila.
A kasar Zimbabwe, kotu ta sallami wani Pasto dan rajin siyasa wanda aka tuhuma da laifin yiwa gwamnatin tsohon shugaba Robert Mugabe zagon kasa.
Shugabannin kasashen nahiyar Afirka da takwarorinsu na turai, suna gudanar da wani taron koli a Abidjan, babban birnin Cote d' Ivoire domin tattauna matsalolin da suka shafi nahiyoyin biyu musamman kan batun kwararar bakin haure zuwa turai.
Sabon gwajin makamin nukiliya da Korea ta Arewa ta yi, ya nuna cewa ta kara inganta makamin ta yadda zai iya tafiya mai nisan zango, lamarin da ya haifar da zaman dar-dar.
Ranar 16 ga watan Nuwamba rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware don karfafa muhimmancin yin hakuri da juna da kuma mutunta juna da ake kira Tolerance Day da turanci.
'Yan gudun hijirar kasar Burundi dake wasu kasashe sun ce suna tsoron kisa, da gana azaba daga dakarun gwamnatin kasar idan suka koma.
Majalissar Dinkin Duniya ta ce mutane miliyan hudu da dubu dari takwas ne ke bukatar agajin jinkai a Sudan, kuma yawancin su suna yankin Darfur.
Zaben shugaban kasar da za a yi gobe Alhamis a Kenya shine karo na biyu a cikin wannan shekarar bayan da kotun kolin kasar ta yi watsi da sakamakon zaben da aka yi a baya, ta ce yana cike da magudi.
Ma’aikatar Lafiya a Najeriya ta ja hankalin masu tafiya jinya a kasashen waje da su yi hattara a saboda yadda ake samun rahotannin likitoci masu satar kodar jama'a, musamman a kasar Masar.
Kungiyoyin kare hakkokin bil'adama sun ce an kashe mutane dayawa a lokutan zanga zanga tun bayan zaben shugaban kasa da aka yi a kasar ta Kenya.
Domin Kari