Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Sudan Zata Sami Agajin miliyoyin Kudade Daga Tarayyar Turai


Majalissar Dinkin Duniya ta ce mutane miliyan hudu da dubu dari takwas ne ke bukatar agajin jinkai a Sudan, kuma yawancin su suna yankin Darfur.

Kungiyar tarayyar Turai ta sanar da shirin bada agajin jinkai na dala miliyan dari da ashirin da hudu ga kasar Sudan.

Majalisar zartaswa ta tarayyar ta fada ranar Litinin cewa za a yi amfani da kudaden agajin wajen samar da bukatun gaggawa, kamar abinci, da ruwa, da tsabtace muhalli, da kiwon lafiya da ilimi, da kuma taimakawa mutanen da akan tilas suka gujewa gidajensu, da kuma garuruwa ko unguwarnin da suka karbe su.

A lokacin da ya kai ziyara kudancin birnin Darfur, ministan ayyaukan jinkai da magance fitinu, Christos Stylianides, ya fadi cewa taimakon agajin na da muhimmanci don taimakawa bukatun ‘yan Sudan da suka rasa muhallansu da ‘yan gudun hijira daga makwabciyar kasar Sudan ta kudu.

Majalissar Dinkin Duniya ta fadi cewa a cikin watan nan kungiyoyin bada agaji sun sami cigaba ta fannnin samun damar kai agaji, musamman a wuraren da ba su sami damar kutsawa ba shekaru da yawa da suka wuce.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG