Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Sallami Wani Dan Rajin Kasar Zimbabwe


Pastor Evan Mawarire#ThisFlag
Pastor Evan Mawarire#ThisFlag

A kasar Zimbabwe, kotu ta sallami wani Pasto dan rajin siyasa wanda aka tuhuma da laifin yiwa gwamnatin tsohon shugaba Robert Mugabe zagon kasa.

Wata mai shari’a a babbar kotu, Priscilla Chigumba ta yanke hukuncin cewa babu wata shaidar dake nuna cewa Evan Mawarire ya nemi a hambarar da gwamnatin Mugabe a shekarar da ta gabata a lokacin da ya jagoranci wata zanga-zanga ta nuna kin amincewa da mulkin dadadden shugaban.

Mawarire, wanda ya kaddamar da wata gwagwarmaya a shafukan sada zumunci mai taken #ThisFlag, ya sanya jerin hotunan bidiyo dake nuna inda yake kira ga jama’a a su zauna gidajensu kada su je aiki ko wuraren sayayya.

Mawarire ya fadawa manema labarai a wajen kotu bayan da aka yanke hukuncin, cewa abin da ya fuskanta wani abu ne da bai dace ba. Ya kuma ce, akwai bukatar mu ga abubuwan da zasu nuna cewa fannin shari’ar kasar zai kasance mai zaman kansa fiye da lokacin gwamnatin da ta shude.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG