Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Zanga Zanga Sun Yi Kone-kone a Pakistan


Masu zanga zanga a Pakistan
Masu zanga zanga a Pakistan

Cikin matsanancin fushi, masu zanga-zanga a Lardin Khyber Pakhtunkhwa da ke Pakistan suka kutsa ofisoshin kungiyoyin mayakan sa-kai da ake zargi da kisan dalibin wata jami’a daga yankin kudancin Waziristan.

Masu zanga-zangar sun kai hari a akalla akan gine-gine biyu da ake zaton na ‘yan Taliban ne a kauyen Sheikh Yousef da ke Gundumar Dera Isma’ila Khan, a arewa maso yammacin Lardin Khyber Pakhtunkhwa.

Bayan kona gine-ginen, masu zanga-zangar sun kuma bankawa motoci da yawa na ‘yan kungiyar wuta.

Mazauna yankin sun maida martanin ne domin kisan wani dalibi da ake kira Idrees, na jami’ar Gomal da ke gundumar Dera Isma’il Khan.

Idrees yana daukan darasi ne a fannin aikin shari’a, wanda suke zargin ‘yan Taliban da kisansa kwanaki biyu da suka wuce.

Koda yake, jami’an lardin sun ce dalibin ya rasa ransa ne sakamakon wata rigima da wasu ‘yan garin, kuma an riga an kama wani da ake zargi yana da hannu a kisan na Idrees.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG