Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya Ta arewa Na Da Niyyar Daina Shirinta Na Makaman Nukiliya Amma Bisa Sharadi


Shugaba Kim Jong-Un da wani jami'i
Shugaba Kim Jong-Un da wani jami'i

Wadannan kalaman na zuwa ne bayan da wani babban wakilin koriya ta kudu ya koma gida daga wata ziyara ta kwanaki biyu zuwa koriya ta arewa inda ya gana da shugaba Kim Jong Un.

Wani jami’in koriya ta kudu ya ce koriya ta arewa ta nuna alamun babu bukatar ta cigaba da shirin ta na makaman nukiliya in aka daina yiwa kasarta barazanar yin amfani da karfin soja, kuma ta nuna alamun za ta hau teburin shawara da Amurka.

Koriya ta arewa ta tabbatar da aniyar dakatar da shirin makaman nukiliya a yankin ruwan koriya, kuma kasar ta ce bata da dalilin da zai sa ta mallaki makaman nukiliya in har an tabbatar mata da tsaron kasarta, an kuma daina yin barazanar amfani da soja,” a cewar Chung Eui-yong babban mai bada shawa ta fannin tsaro a Koariya ta kudu, a lokacin da yake magana da manema labarai a birnin Seoul.

Chung ya ce koriyoyin biyu sun amince za su yi wani babban taro karon farko tun bayan fiye da shekaru 10 da suka gabata a watan Afirilu. Ya kuma kara da cewa koriya ta arewa ta ce ta yi na’am da yin tattaunawa akan dakatar da shirin makaman nukiliya da kuma gyara dangantakar dake tsakaninta da Amurka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG