Alkali Abang ya ce albashi da sauran alawus-alawus din Maina bai isa ya kai ga tara wadannan kudade ba.
Izuwa lokacin hada wannan rahoto, an kidaya kananan hukumomi tara. cikin 21 da jihar ta Anambra ke da su.
“Ina so na sanar da ku cewa wannan murabus da na yi, na yi shi ne bisa radin kaina. Ina kuma godiya ga gwamna Yahaya da ya ba ni wannan damar ta yin aiki a gwamnatinsa.” In ji Dr Hussaina
Sakamakon wannan wasa ya ba City damar matsawa zuwa matsayi na biyu a teburin gasar ta Premier.
Babu dai wani rahoto da ya nuna cewa an samu wata tangarda ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, illa ‘yar matsalar na’ura da aka samu a wasu rumfunan zabe a sassan jihar.
Farfesa Osinbajo ya ce ya mika wannan batu ga lauyoyinsa don su dauki matakin da ya dace.
Ya zuwa yanzu, mutum tara aka ceto da ransu, mace daya da maza takwas a cewar hukumomin jihar ta Legas.
Kazalika kungiyar ta PSG ta bayyana cewa Marco Verratti, shi ma bai zai buga wasan ba, saboda yana kan murmurewa daga wata jinya.
Har ya zuwa yanzu ba a san iya adadin mutanen da ke cikin ginin ba a lokacin da ya fadi amma ana fargabar akwai akalla mutum 50 a c
Rahotanni sun ce daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su akwai Farfesoshi biyu da wasu daga cikin iyalansu.
Ruftawar gine-gine a jihar Legas da ke kusa da teku, abu ne da ya sha faruwa inda a lokuta da dama akan dora alhakin hakan akan masu gine-gine da ke amfani da kayan gini marasa inganci.
A ranar Talata 2 ga watan Nuwamba Buhari zai gabatar da jawabinsa a gaban taron kamar yadda wata sanarwa da kakakinsa Malam Garba Shehu ya fitar ta ce.
“Mun fuskanci kalulabe a baya, amma ga duk wanda yake so ya sani, PDP ta dawo – PDP ta dawo don ta ceto Najeriya daga kangin da muka shiga cikin shekaru shida.” Ayu ya ce.
A ranar 29 ga watan Mayun 2023, Buhari zai kammala wa’adin mulkinsa na biyu.
Wannan mataki na sauya sunan na zuwa ne yayin da kamfanin ke fuskantar wasu kalubalen da suka shafi zargin da ake masa na fifita riba akan kare masu amfani da shafin.
A ranar Litinin Buhari ya isa birnin Riyadh don halartar taron koli na saka hannun jari bisa gayyatar Sarki Salman Abdulaziz Al Saud.
Cikin wata sanarwa da ya fitar, Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya yaba da sakin Hamdok inda ya ce har sun gana da shi.
Domin Kari