Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya nuna alhininsa dangane da asarar rayukan da ake yi a kasar, yana mai Allah wadai da masu kai hare-hare akan jama'ar da ba su ji ba ba su gani ba.
Atiku ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook yana mai cewa abin da ke faruwa a Najeriya abu ne na bakin ciki.
“Abu ne mai karya zuciya da baƙanta rai yadda a yau a ƙasarmu ran ɗan adam ba ya bakin komai.
“Dole a la'anci kashe mutane haka siddan da ake yi kusan kullum a ƙasar nan.” Atiku Abubakar ya ce bayan hare-haren da ‘yan bindiga suka kai jihar Kaduna wanda ya halaka mutane da dama.
Atiku Abubakar wanda shi ya tsayawa babbar jam’iyyar adawa ta PDP takarar shugaban kasa a zaben 2019 ya kuma mika ta’aziyyarsa ga wadanda hare-haren suka shafa.
“Ina addu'a da jajantawa iyalan waɗanda hare-haren kananan hukumomin Giwa, Chikun, Zaria da Zangon Kataf na jihar Kaduna suka rutsa da su. Ina Addu'ar samun jinƙan Ubangiji gare su." In ji Atiku.
Rahotannin bayan-bayan nan sun ce akalla mutum 38 suka rasa rayukansu a kauyukan da aka kai hare-hare a jihar ta Kaduna a karshen makon da ya gabata.