Dan wasan Barcelona Sergio Aguero ya ce bait aba mafarkin zai taka kwallo a nahiyar turai a lokacin da yake burin ya zama dan wasan kwallon kafa.
Aguero ya bayyana hakan ne a Camp Nou yayin da yake jawabin ban kwana da kuma yin ritaya daga buga kwallo.
“Lokacin da na fara taba kwallo, burin a shi ne buga wasa a babbar gasa, amma tunanina bait aba kai wag a zan buga wasa a turai ba.” In ji Aguero wanda dan asalin Argentina ne.
Gwaje-gwajen da aka yi wa Aguero bayan da ya samu matsalar numfashi yayin da yake wasa sun gano cewa yana fama da matsalar zuciya.
Hakan ya sa yanke shawarar yin ritaya domin kula da lafiyarsa.
“Ina so na mika godiya ta ga kungiyar Atletico Madrid da suka fara ba ni dama buga musu kwallo tun ina shekara 18.
“Ga wadanda suke kungiyar Manchester City, kusan yadda nake ji da wannan kungiya, na yi iya bakin kokari na, sai kuma Barcelona wacce ta karbe ni hannu bibiyu.” Aguero ya fada cikin hawaye.
A lokacin bazara Aguero ya koma Barcelona bayan da ya kwashe shekaru da dama a kungiyar Manchester City.
Dan shekara 33, Aguero ya fice a filin wasa a ranar 30 ga watan Oktoba a lokacin karawarsu da Alaves a gasar La Liga, inda ya rke kirjinsa yayin da yake ficewar.