Ofishin da ke kula da basussukan da ake bin Najeriya na DMO ya ce adadin bashin da ake bin kasar a ciki da wajen gida ya kai Naira tiriliyan 38.05, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 92.6.
A cewar ofishin, wannan adadin bashi shi ne wanda ake bin Najeriya ya zuwa karshen zangon shekara na uku da yak are a ranar 30 ga watan Satumbar bana.
Ofishin ya kara da cewa basukan sun hada da wanda gwamnatin tarayya, jihohi 36 da birnin tarayya na Abuja suka ciyo.
Hakan na nufin an ga karuwar bashin da naira tiriliyan 2.5 idan aka kwatanta da naira tirilyan 35.4 da ake bin kasar a karshen zangon shekara na biyu.
“Dalilin karin da aka gani a basukan da ake bin Najeriyar, na da nasaba da kudaden takardu masu daraja na (bonds) wadanda yawansu ya kai dalar Amurka biliyan hudu da gwamnatin tarayya ta fitar don karbo basukan.”
“Sai dai fitar da kudaden takardun masu daraja (don karbo basukan) ya yi rana ga tattalin arzikin Najeriya domin ya kara adadin kudaden da Najeriya ke ajiyewa a waje, abin da ya taimakawa musayar kudaden da ake yi da naira da kuma samar da kudaden da gwamnati ke gudanar da manyan ayyukan da ke cikin kasafin kudin kasar.” Sanarwar da ofishin na DMO ya fitar ta ce.