Sai dai sanarwar ba ta bayyana dalilin rusa majalisar zartarwar ba, amma ta ce nan ba da jimawa ba za a sake kafa wata majalisar.
Wannan yajin aiki ka iya haifar da matsalar karancin man a yankin arewacin kasar ciki har da Abuja, babban birnin Najeriya kamar yadda masu lura da al'amura suka bayyana.
A wani taron kasa da aka kaddamar da shirin yaki da masu aikata manyan laifuka wanda ya gudana a jihar Pennsylvania, Biden ya takawa ‘yan Republican burki kan kalaman da suke yi, wadanda ya ce ba su dace ba.
Ita dai jam'iyyar APC mai mulki ta ce lokaci kawai take jira ta lashe zaben wanda za a yi a watan Fabrairun badi.
“Ba za kuma mu manta da yadda Gorbachev ya yi ta yekuwar tarayyar Soviet da Amurka su rusa makaman nukiliyansu ba, a lokacin wani zama da suka yi da tsohon shugaban Amurka Ronald Reagan.”
Akalla ‘yan sanda hudu aka kashe a farkon watan Agusta a jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya, a wani hari da ake zargin ‘yan aware ne suka kai.
“Da ma mu akidarmu, duk inda za a yi zalunci, babu adalci, babu mu a wurin. Da a ce kawai wata bukatata ce ko bukatar wasu daga cikin wadanda muke shugabanci tare da su, ai da wannan gayyar ta al’umar Kano, da ba su mana biyayya ba.” In ji Shekarau
Kaddamar da ofishin jami'yyar na zuwa ne, kwanaki uku bayan da rahotanni suka nuna cewa ‘yan sanda a jihar sun rufe ofishin na NNPP da ke garin Maiduguri.
Wannan lamari ya sa ana tunanin Trump ya karya doka kuma zai iya fuskantar tuhuma a kotu yayin da lauyoyinsa suka nemi wata kotu ta dakatar da nazarin da ake yi kan takardun.
Cikin wani sako da ya wallafa a watan Yuni a shafinsa na Twitter, Atiku ya tabbatar da cewa jam’iyyar tana kokarin dinke barakar da ta kunno kai a jam'iyyar, yana mai cewa, za a sasanta komai.
A watan Yulin da ya gabata, Osinbajo ya sanar da cewa an yi masa tiyata a kafa sanadiyyar wani ciwo da ya ce ya jima yana fama da shi.
“NFF ba ta da hannu a wannan akasi da aka samu, domin ta shirya tsaf don tarbar tawagar ‘yan wasan a Abuja, gabanin a samu tangarda a tafiyar ta su.” In ji Sanusi.
Mai magana da yawun Osinbajo, Laolu Akande, wanda ya tabbatar da lamarin, ya ce, likitocinsa za su yi karin bayani a nan gaba.
Shirin har ila yau, ya duba kiran da hukumomin Amurka suka yi ga jama’a da su yi hattara yayin da aka samu bullar wasu na’ukan cutar ta COVID da suke da saurin yaduwa.
Kasashen Australia da New Zealand ne za su karbi bakuncin gasar ta cin kofin duniya ta mata a badi.
Davido na da mabiya miliyan 11.8 a dandalin Twitter yayin da a Instagram yake da mabiya miliyan 24.6.
PDP ta shigar da karar ce a wata babbar kotu da ke Abuja, babban birnin Najeriya.
Shirin har ila yau, ya yi duba kan wani sabon rahoto da aka fitar, wanda ya kara tabbatar da cewa 'yan sandan garin Uvalde a jihar Texas, sun yi sakaci wajen kai dauki yayin da wani dan bindiga ya shiga wata makarantar firamare ya harbe yara 19 da malamai biyu a watan Mayu.
A ranar 5 ga watan Yuli, wasu ‘yan bindiga suka far wa gidan yarin na Kuje da ke babban birnin tarayyar Najeriya, suka kubutar da mutane da dama, ciki har da fursunonin da ake zargin mayakan Boko Haram ne.
Obi ya kuma nuna kwarin gwiwar cewa Baba-Ahmed zai yi amfani da dumbin iliminsa wajen ganin an cin ma burin da suka sa a gaba na ‘Rescue Nigeria Project’ – wato shirin kubutar da Najeriya don a kyautata makomarta.
Domin Kari