Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Osun: Yadda Davido Yake Taya Kawunsa Kamfen


Davido (tsakiya) Ademola Adeleke (sanye da shudiyar hula) (Facebook/PDP)
Davido (tsakiya) Ademola Adeleke (sanye da shudiyar hula) (Facebook/PDP)

Davido na da mabiya miliyan 11.8 a dandalin Twitter yayin da a Instagram yake da mabiya miliyan 24.6. 

Fitaccen mawaki afrobeat a Najeriya David Adeleke wanda aka fi sani da Davido ya taya kawunsa kamfen a gangamin yakin neman zaben gwamna da za a yi a jihar Osun da ke kudu maso yammcin kasar.

A ranar Asabar 16 ga watan Yuli za a yi zaben gwamna a jihar ta Osun don zaben wanda zai mulki jihar nan da tsawon shekaru hudu masu zuwa.

Davido na da mabiya miliyan 11.8 a dandalin Twitter yayin da a Instagram yake da mabiya miliyan 24.6.

Gwamna Adegboyega Oyetola na jam’iyyar APC mai mulki, wanda ke neman wa’adi na biyu, zai fafata da dan takarar jam’iyyar PDP, Sanata Ademola Adeleke.

Adeleke, dan shekara 61, wanda kawu ne ga Davido, ya taba wakiltar yammacin jihar ta Osun a majalisar dattawan Najeriya.

A ranar Alhamis jam’iyyar ta PDP ta gudanar da babban gangaminta na neman goyon bayan al’umar jihar ta Osun a Osogbo, babban birnin jihar, wacce jam’iyyar APC ta kwashe wasu shekaru tana mulka.

Taron gangamin ya samu halartar dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar ta PDP Atiku Abubakar da dan takarar mataimakin shugaban kasa, gwamnan jihar Delta Infeanyi Okowa.

Baya ga Oyetola da Adeleke, akwai dan takarar jam’iyyar SDP Omigbodun Oyegoke Oyegoke Akinnrinola da shi me yake neman kujerar.

Hukumar zabe ta INEC ta nuna cewa ‘yan takara 15 ne suke neman kujerar ta gwamna.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG