Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kurar Da Batun Ganawar Tinubu Da Wike Ta Tayar A Fagen Siyasar Najeriya


Bola Tinubu, hagu, Nyesom Wike, dama (Facebook/Instagram: Bola Tinubu/Nyesome Wike)
Bola Tinubu, hagu, Nyesom Wike, dama (Facebook/Instagram: Bola Tinubu/Nyesome Wike)

Cikin wani sako da ya wallafa a watan Yuni a shafinsa na Twitter, Atiku ya tabbatar da cewa jam’iyyar tana kokarin dinke barakar da ta kunno kai a jam'iyyar, yana mai cewa, za a sasanta komai.

Rahotanni daga Najeriya na nuni da cewa Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike da dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu sun yi wani zama a birnin London.

Ganawar gaggan ‘yan siyasar biyu ta wakana ne yayin da duk yunkurin da aka yi ta yi na ganin an sasanta bangaren dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP Atiku Abubakar da Wike ya ci tura.

Wike ya zo na biyu a zaben fitar da gwani na mukamin shugaban kasa karkashin jam’iyyar adawa ta PDP.

Rahotannin da wasu manyan kafafen yada labaran Najeriya suka ruwaito, sun nuna cewa tawagar da Wike ya je da ita wajen ganawar ta Lodnon, ta hada da gwamnan jihar Benue Samuel Ortom, gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde da kuma gwamnan Abia Ikpeazu Okezie.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar

A bangaren Tinubu kuma, akwai Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti da Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas.

Babu cikakkiyar masaniya game da abin da ganawar ta kunsa, amma majiyoyi kwarara da wasu manyan kafafen yada labaran Najeriya irinsu Daily Trust, Vanguard da Punch suka ruwaito, sun nuna cewa batun zaben 2023 shi ne ya mamaye taron.

Yadda Korafin Wike Ya Samo Asali

A watan Mayu, Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya lashe zaben fitar da gwani a jam’iyyar PDP inda daga baya ya dauki gwamnan jihar Delta Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakinsa.

Kamar yadda rahotanni suka nuna, wannan al’amari bai yi wa Wike dadi ba, hakan kuma ya sa ya fito fili yana ta nuna adawarsa ga mahukuntan jam’iyyar ta PDP.

Ko da yake, Wike kan fake da batun neman shugaban jam’iyyar ta PDP Dr. Iyorchia Ayu ya yi murabus daga mukaminsa a matsayin korafinsa na zahiri, domin a cewar Wike, Ayu ya yi alkawarin zai sauka idan har dan arewa ya samu tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar.

Lokacin da aka zabi Ifeanyi Okowa, hagu, a matsayin abokin takarar Atiku, dama (Hoto: Facebook/PDP)
Lokacin da aka zabi Ifeanyi Okowa, hagu, a matsayin abokin takarar Atiku, dama (Hoto: Facebook/PDP)

Amma a badini, kamar yadda masu sharhi ke nunawa, rashin samun gurbin mataimakin shugaban kasa ne asalin damuwarsa – duba da cewa shi ne ya samu kuri’a mafi yawa bayan Atiku.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a tsakiyar Agusta, mai magana da yawun Dr. Ayu, Siomon Imobo-Tswam ya ce “Ayu ba zai yi sauka a mukaminsa ba, har sai ya kammala wa’adin shekaru hudu da doka ta tanada masa.”

Manya daga cikin jam’iyyar ta PDP, ciki har da Atiku sun yi ta yunkurin ganin an rarrashi Wike.

Cikin wani sako da ya wallafa a watan Yuni a shafinsa na Twitter, Atiku ya tabbatar da cewa jam’iyyar tana kokarin dinke barakar da ta kunno kai a jam'iyyar, yana mai cewa, za a sasanta komai.

“Muna daukan matakan magance korafe-korafe dukkan mambobin jam’iyya. Hadin kanmu shi ne muhimmin abu a gare ni.” In ji Atiku.

Sai dai wasu masu sa ido kan harkar siyasar Najeriya, na da ra’ayin cewa, bangaren na Atiku, ya yi jinkiri wajen lallamin gwamnan na Rivers.

Waiwaye Kan Rahotannin Haduwar Wike Da ‘Yan APC A Baya

Idan za a iya tunawa, a farkon watan Yuli, wasu Gwamnoni APC sun kai wa Wike ziyara a wani abu da ake ganin yunkuri ne na janyo hankalinsa zuwa jam’iyyar mai mulki.

Gwamnonin sun hada da Fayemi na jihar Ekiti, Sanwo-Olu na jihar Legas da kuma Rotimi Akeredolu na jihar Ondo - dukan su gwamnoni daga kudancin Najeriya.

Fayemi da Sanwo-Olu, na cikin wadanda aka yi ganawar London da su kamar yadda rahotanni suka nuna.

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu (Facebook/Gwamna Sanwo-Olu)
Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu (Facebook/Gwamna Sanwo-Olu)

Wannan ziyarar da gwamnonin suka kai wa Wike a wancan lokaci, na zuwa ne kwanaki kadan bayan rahotanni da suka karade sassan Najeriya cewa, Wike ya kai wa Tinubu ziyara a Paris – ko da yake dukkan bangarorin biyu sun musanta wannan haduwa.

“Ya kamata mu fayyace wannan lamari, duk da cewa Asiwaju Tinubu yana Faransa a yanzu, bai yi wata ganawa da Gwamna Wike ba a wannan kasa.” Mai magana da yawun Tinubu, Tunde Rahman ya fada cikin wata sanarwa da ya fitar, wacce jaridar Premium Times ta wallafa a ranar 1 ga watan Yuli.

Abin Da Masu Sharhi Ke Cewa

Ko da yake, kusan sama da sa’a 24 kenan da bullar labarin haduwar Tinubu da Wike a London, amma ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu wani bayani da ya fito daga bangarorin biyu da ke musanta wannan haduwa.

Hakan ya saba bayyanar labarin cewa ‘yan siyasar biyu sun hadu a Faransa, wanda suka yi wuf suka musanta.

Kazalika hakan ya bude kofar tsokaci daga masu sharhi kan al’amuran siyasar ciki da wajen Najeriya.

Yayin da masu sharhi irinsu Samuel Akinwale, ke nuni da cewa zai yi wuya Wike ya amince ya bi ‘yan APC, wasu kuwa na ganin kamar an yi an gama, duba da yadda bangarorin biyu suka bari labarin ya fita.

Wani gangami da jam'iyyar PDP a Najeriya (Hoto: Facebook/PDP)
Wani gangami da jam'iyyar PDP a Najeriya (Hoto: Facebook/PDP)

“Ina ga zai yi wuya Wike ya shiga APC, dalilina kuwa shi ne, APC ba za ta iya ba shi abin da ya rasa a PDP ba.

“Abu na biyu shi ne, mafi aksarin mutanen da ke tawagar Wike a PDP, irinsu Gwamna Makinde da Ortom na jihar Benue, duk sun riga sun samu tikitin yin takara, misali, Makinde ya samu tikitin neman wa’adi na biyu, Ortom ya samu tikitin tsayawa takarar sanata, sannan wanda Wike yake so ya gaje shi, shi ma ya samu tikitin tsayawa takara a jihar Rivers- dukkansu karkashin jam’iyyar PDP.

“Saboda haka, ban yi tsammanin wadannan mutane duk za su sadaukar da wannan nasarori na su ba.” In ji Akinwale.

Wasu har ila yau na ganin, Wike na rabar APC ne saboda ya karawa kansa daraja a idon PDP don ya samu biyan bukatarsa cikin sauki.

Sai dai wasu masu sharhi kan siyasar Najeriya na ganin, Wike zai yada zango a APC a karshe, domin a cewarsu, halayyarsa ta hawa dokin na-ki, ta sa gwamnonin yankin kudu maso kudancin Najeriya suna dari-dari da shi.

Sannan, Wike, kamar yadda ake cewa, ya lura cewa, mai yiwuwa, ‘yan arewa za su marawa dan takarar da ya fito daga yankinsu baya ne a zaben na 2023, shi ya sa ya gwammace shi ma ya karkata hankalinsa kan dan takarar da ya fito daga yankinsa, dalili kenan da ake ganin yana rabar Tinubu.

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido yayin wata ziyara da ya kawo VOA a Washington
Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido yayin wata ziyara da ya kawo VOA a Washington

Sai dai da yawa daga cikin manyan ‘yan jam’iyyar ta PDP, irinsu tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido, na ganin Wike ba shi da tagomashin da zai iya yin mummunan tasiri akan jam’iyyar.

“Wike mutum ne fa, don ya kasance gwamnan jihar Rivers hakan bai zama cewa shi ya mallaki al’umar jihar Rivers ba.

“Ya kamata mu manta da shi….. nan da wasu watanni takwas za a manta da shi kamar yadda aka manta da ni.” Lamido ya ce, a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels.

Yayin da wasu da dama ke ganin mai yiwuwa PDPn ta yi biris da batun haduwar Wike da Tinubu – ta ce Allah raka taki gona, wasu kuwa gani suke, suna can suna share zufa domin hakan zai iya dama musu lissafi.

Shin Wike zai koma APC? shin zai ci gaba da zama a PDP? Wane tasiri ficewar shi ko zaman shi PDP zai yi a zaben 2023?, wadannan wasu tambayoyi ne da lokaci ne kadai zai fayyace su.

XS
SM
MD
LG