Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gorbachev Ya Ba Da Gudunmowa Sosai Wajen Tabbatar Da Zaman Lafiya A Duniya - Buhari


Shugaba Buhari (Facebook/Bashir Ahmad)
Shugaba Buhari (Facebook/Bashir Ahmad)

“Ba za kuma mu manta da yadda Gorbachev ya yi ta yekuwar tarayyar Soviet da Amurka su rusa makaman nukiliyansu ba, a lokacin wani zama da suka yi da tsohon shugaban Amurka Ronald Reagan.”

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya jinjinawa tsohon shugaban Tarayyar Soviet, marigayi Mikhail Gorbachev, bisa irin rawar da ya taka wajen dabbaka zaman lafiya a duniya a lokacin yana raye.

Buhari ya yabi shugaban tarayyar ta Soviet na karshe ne yayin da yake mika sakon ta’aziyyarsa bayan rasuwar Gorbachev.

A ranar Talata Gorbachev, wanda shi ne shugaban tarayyar ta Soviet na karshe, ya rasu a wani asibiti da ke Moscow. Shekarunsa 91.

Marigayi Gorbachev
Marigayi Gorbachev

“Tarihin da ya bari, ba abu ne da ya shafi tsohuwar tarayyar ta Soviet kadai ba, abu ne da ya shafi duniya baki daya, kamar yadda ya sa aka wargaza yarjejeniyar rundunar hadin gwiwar soji ta Warsaw, da zimmar ganin an samar da zaman lafiya a duniya.

“Ba za kuma mu manta da yadda Gorbachev ya yi ta yekuwar tarayyar Soviet da Amurka su rusa makaman nukiliyansu ba, a lokacin wani zama da suka yi da tsohon shugaban Amurka Ronald Reagan.” Wata sanarwa da kakakin Shugaba Buhari, Malam Garba Shehu ya fitar ta ce.

“Ko da yake, Gorbachev ya mutu ba tare da ya cin ma burinsa na ganin an kawar da makaman nukiliya a doron kasa ba, amma yadda ya kuduri aniyar tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya, abu ne da ba za a taba mantawa da shi ba.” Buhari ya kara da cewa.

XS
SM
MD
LG