A karon farko tun bayan da aka yi masa tiyata, Mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, a ranar Laraba ya halarci taron majalisar zartarwa a zahiri.
A watan Yulin da ya gabata, Osinbajo ya sanar da cewa an yi masa tiyata a kafa sanadiyyar wani ciwo da ya ce ya jima yana fama da shi.
Wani hoto da aka wallafa a shafinsa na Facebook a watan Yuli, ya nuna mataimakin shugaban kasar rike da sanda tare da mai dakinsa da kuma wasu ma'aikatan lafiya.
A lokacin da yake jinyar, mataimakin shugaban kasar kan halarci taron majalisar zartarwar ne da wasu taruka ta kafar yanar gizo.
Yayin zaman taron wanda ya gudana a fadar shugaban kasa a ranar Laraba a Abuja, an ga ministoci da sauran ma’aikatan fadar suna ta yi wa Osinbajo barka da dawowa.
Kamar yadda aka saba a duk lokacin da yake kasa, Shugaba Muhammadu Buhari ne ya jagoranci zaman majalisar zartaswar.