Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu 'Yan Siyasa Na Dumama Yanayi Da Laffuzan Su Yayin Gangamin Neman Zabe-Kwararru


Kwamiti wadda ke karkashin jagorancin farfesa Ibrahim Umar ya bayyana damuwa da kakkausan harshe game da yadda wasu daga cikin shugabanin siyasa a Kano ke kokarin dumama yanayi a jihar ta hanyar furta kazaman kalamai da ka iya tunzura magoya baya

Kwamitin wanzar da zaman lafiya a jihar yayin zabuka yace yana aikin tsara wani taron masu ruwa da tsaki da shugaban kwamitin zaman lafiya na kasa Janar Abdussalami Abubakar zai jagoranta a Kano. Sai dai kwamitin ya gargadi shugabanin Jam’iyyun siyasa da ‘yan takara a mataki daban daban su kiyaye laffuzan su yayin tarukan neman kuri’ar Jama’a.

Comrade Ibrahim Abdullahi Wayya dake kula da ayyukan sakatariyar kwamitin yace, shugabancin kwamitin ya bukaci hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki su tashi tsaye sosai.

“Kalmar tsiya-tsiya da shugaban Jam’iyyar APC na Kano Abdullahi Abbas yayi amfani da ita a yayin taron su na kamfe da kuma martanin makamanciyar wannan kalma da shugaban NNPP na Umar Haruna Doguwa ya furta a makon jiya, na daga cikin laffuzan da suka daga hankalin wannan kwamiti, domin kuwa kalamai da ka iya tada fitina a tsakanin al’uma ne” inji Comrade Wayya.

Gargadin kwamitin na zuwa ne a dai-dai lokacin da shugaban Jam’aiyyar APC a Kano ke karin haske akan abinda yake nufi da wadancan kalamai nasa. “Kalmar tsiya-tsiya ba bindiga ba ce, ba takobi ba ne kuma ba kibiya ba ce, don haka kalma ce dake nuna bukatar jajircewa ga magoya baya, kuma duk bahaushe ya san abinda ake nufi kalma ce ta ‘yan siyasa ga ‘yan siyasa." inji Abdullahi Abbas, shugaban APC na Kano.

Tuni dai masu kula da lamura ke da ra’ayin cewa, gargadin da kwamitin zaman lafiyar na Kano a wannan gaba, tamkar fargar jaji ne, la’akari da yadda wadancan lafuza suka fara mummunan tasiri. Sai dai Comrade Ibrahim Abdullahi Wayya yace ba haka lamarin yake ba domin kuwa kwamitin ya dauki dogon lokaci yana taruka da masu ruwa da tsaki akan al’amuran gudanar da zabe cikin tsafta da nasara. Kuma a yanzu haka yana shirye-shiryen gudanar da taron kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin ‘yan takara wadda shugaban kwamitin zaman lafiya na kasa Janar Abdussalam Abubakar zai jagoranta.

Saurari rahoto cikin sauti:

Kwamitin wanzar da zaman lafiya na Jahar Kano.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG