Dangane da haka ne babban Daraktan hukumar Alhaji Faruk Salim ya jagoranci tawagar Jami’an sa, zuwa kasar Turkiyya, inda suka halarci babban taron kasa da kasa kan harkokin tsarin sarrafawa da cinikayyar kayayyaki na tafarkin Halal wadda ya gudana a birnin Santanbul a kwanakin baya.
Darktan Ofishin shiyyar Kano na hukumar kula da Ingancin kayayyakin ta Najeriya, Mr Albert Wilberforce wanda ke cikin ‘yan tawagar, yace ana bar Najeriya a baya, musamman la’akari da yadda ake hada hadar biliyoyin Dala a kasuwannin duniya bisa wannan tsari na Halal. Yace la’akari da yawan al’umar Musulmi dake Najeriya, musamman jihar Kano, ya sanya shugabancin hukumar ta S.O.N ya kara kaimi wajen ganin cewa, Najeriya ta shiga an dama da ita ta wannan fuska.
A cewarsa, daga nan zuwa watan Afrilun badi ne ake sa ran Najeriya zata iya cika sharrudan samun rijistar shiga jerin kasashen duniya masu cinikayya bisa tafarkin halal.
Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da hukumar ta SON ta bada lambar shaidar ingancin kayayyaki guda 102 ga kamfanoni daban daban a Kano, da hakan ke nuna ta aminta da yadda suke gudanar da ayyukan sarrafa kayayyaki a masana’antu su.
Ko da yake hakan na faruwa ne adai-dai lokacin da al’uma ke ci gaba da nuna damuwa kan yawaitar kayayyakin jabu a kasuwannin Kano, amma Alhaji Sambo Iliyasu daraktan ayyuka na musamman a hukumar kare hakkin mai saya da mai sayarwa ta jihar Kano yace wasu gurbatattun mutane ne ke kwaikwayon kayayyakin da wasu kamfanonin ke sarrafawa, suna yin jabunsu.
Hukumar ta tashi tsaye wajen murkushe ayyukan irin wadannan bata gari, ta hanyar kama su da kuma gurfanar da su a gaban shari’a. Yace yanzu haka Majalisar dokokin jihar Kano na kokarin yin garanbawul ga dokar da ta kafa hukumar tasu, domin ta zama mai zaman kanta ta yadda zata kara samun karfin iko da kuma fadada aikace-aikacen ta da-ma samar da larin ofisoshi da ma’aikata.
Masu kula da lamura dai na ganin, gurbatattun ‘yan kasuwa na neman mayar da Kano cibiyar hada-hadar cinikayyar kayayyakin Jabu, lamarin dake barazana ga lafiyar al’umma.
Saurari rahoton cikin sauti: