Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Martanin ‘Yan Najeriya Kan Rahoton Hukumar NBS Da Ya Ce Mutum Miliyan 133 Na Cikin Kangin Rayuwa A Kasar


Wasu ‘yan Najeriya.
Wasu ‘yan Najeriya.

Kwararru kan harkokin tattalin arziki da masana kimiyyar halayya da zamantakewar dan adam a Najeriya da kuma talakawan kasar sun fara mayar da martani akan alkaluman da hukumar kula da lamuran kididdiga da bincike kan sha'anin ci gaba ta kasar, wato National Bureau for Statistics NBS ta fitar a makon jiya game da mizanin talauci da 'yan Najeriyar ke fuskanta.

Alkaluman na kunshe ne cikin wani rahoto da hukumar ta NBS ta wallafa a ranar alhamis ta makon jiya, wadda ya nuna daga cikin kiyasin yawan ‘yan Najeriya miliyan 200, fiye da miliyan 133 na cikin kangin rayuwa saboda tsananin talauci.

Daga cikin wannan adadi in ji rahotan, mutane miliyan 86 mazauna yankin aewacin Najeriya ne.

Wata mota dauke da jama’a tayi kokarin arcewa daga tashe-tashen hankula a birnin Maiduguri.
Wata mota dauke da jama’a tayi kokarin arcewa daga tashe-tashen hankula a birnin Maiduguri.

Rahotan ya biyo bayan wani kwarya-kwaryan bincike ne na tsawon shekara guda da hukumar ta NBS ta yi a jihohi 36 da yankin Abuja bisa hadin gwiwa da wasu hukumomin ketare da suka hada da UNICEF da UNDP.

A hira da wakilinmu a Kano, wasu ‘yan Najeriya sun bayyana ra’ayoyinsu dangane da wannan rahoto na hukumar NBS.

Malam Musa Mohammed wani magidanci ne mai sana’ar gine-gine ya ce shi a fahimtar adadin mutanen da suke fama da matsalolin rayuwa saboda talauci a Najeriya ya zarce abin da ke cikin rahotan hukumar ta NBS la’akkari da dinbin kalubalen rayuwa da ‘yan kasar ke fuskanta.

“‘Yaya na 14, mata ta guda daya. A shekaru 10 zuwa 15 da suka wuce na kan saya ko na noma abin da zan ci da iyali tsawon shekara guda da rabi, amma yanzu ba ni da kudin da zan iya sanyen kwano guda na hatsi. Yanzu haka ina da yara 2 kwance a gida ba su da lafiya, amma ba ni da kudin da zan kai su asibiti” In ji Malam Musa Mohammed.

Shi-ma Malam Isma’ila Danbatta ya kara tabbatar da alkaluman da hukumar ta NBS ta wallafa.

“Ina cikin wadancan mutane miliyan 133 da wannan hukuma ta ambata, domin kuwa ni ina da sana’ar hannu, amma na sahafe kimanin makonni uku ba na samun aiki. Rayuwa ta yi wuya, ga tsadar kayayyakin masarufi, ga kuma tarin iyali da ‘yan uwa, shugabanni da attajirai ba sa taimakawa na kasa, kawai su dai daga su, sai ‘yayan su, uwa da kuma matansu” Malam Isma’ila Danbatta ya ce.

Magidanta dubu 56 ne aka tattauna da su kan yanayin rayuwa a fannoni daban-daban a yayin binciken, inda sakamakon ya nuna, mazauna jihar Sokoto na kan gaba wajen fuskantar wannan kalubale.

Unguwar Oyingbo a jihar Legas (Reuters)
Unguwar Oyingbo a jihar Legas (Reuters)

Dr Abdulrazak Ibrahim Fagge, masanin tattalin arziki a Jami’ar Bayero Kano ya ce, baya ga kalubalen tsaro da karancin masana’antu a galibin jihohin arewacin Najeriya, tsarin biyan harajin VAT na amfani da kayayyaki da ake baiwa jihohin Lagos da Ogun da sauran su, maimakon a biya a wurin da mutane suke sayan kayayyakin domin amfani, wato kamar Kano, Sokoto ko Zamfara ya na daga cikin karin matsaloli da suka jefa lardin na arewa a cikin wannan hali.

A nasu bangaren, masu nazari akan kimiyyar halayya da zamantakewar bil’adama sun ce rahotan na hukumar NBS ya kara haska yadda talauci ke barazana ga tsarin zantakewa a tsakanin ‘yan Najeriya.

Farfesa Abdullahi Maikano Madaki, masanin kimiyyar Halayya da zamantakewar dan Adam a Jami’ar Bayero, Kano ya ce zurfin talauci a kasa na haifar da yanayin rashin yarda da aminci a tsakanin al’uma, baya ga karuwa aikata miyagun laifuka a kasa.

Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:

Martanin ‘Yan Najeriya Kan Rahoton Hukumar NBS Da Ya Ce Mutum Miliyan 133 Na Cikin Kangin Rayuwa A Kasar - 3'38"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:38 0:00

XS
SM
MD
LG