Yayin da al’umar musulmi ke daf da kammala ibadar Azumin Ramadana, aiwatar da shirin gwamnatoci na ciyar da mabukata a cikin wannan wata na cin karo da kalubalen zargin almundahana, inda ake tuhumar wasu daga cikin Jami’an gwamnati da hannu.
Daruruwa kananan kungiyoyin manoma da masu sana’ar casar shinkafa da gyaran sauran kayayyakin noma a garuruwa da kayuka daban-daban na yankin arewacin Najeriya zasu ci gajiyar tsarin bada rancen kudi da babu ruwa na bankin duniya wadda aka kaddamar a jihar Jigawa.
'Yan fansho a jihar Kano sun bukaci hukumar kula da asusun fansho ta jihar ta hanzarta sayar da gidajen da hukumar EFCC ta karbo musu, wadanda gwamnatin jihar ke rike da su fiye da shekaru goma da suka gabata.
A yau Talata ne shugaban kwamandan Hisbah ta jihar Kano Mal Aminu Ibrahim Daurawa ya koma bakin aikinsa biyo bayan murubus da yayi a makon da ya gabata bayan wani jawabi da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf yayi a gidan gwamnati yayin da yake ganawa da Malaman Addini.
A ci gaba da daukar mataki da dan adam ke yi kan sauyin yanayi da illolinsa, wata kungiya, da hadin gwiwar jihohin arewa maso yammacin Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki, sun hadu a birnin kano, don neman mafita ta bai daya.
Kamen masu aikata badala a wasu sassa na birni da kewayen Kano da damkewa tare da gurfanar da matashiyar nan da ke kalaman batsa Murja Kunya a kotu, na daga cikin abubuwan da suka sabbaba wannan takaddama.
Majalisar dokokin Kano ta yi karin haske dangane da mabanbantan wasikun da take karba daga kungiyoyi masu neman a sake fasalin dokar data kafa masarautun jihar guda biyar, sai dai masana na cewa, bada damar jefa kuri’ar raba gardama zai taimaka wajen waware wannan batu cikin ruwan sanyi.
Hukumar NDLEA mai hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya, ta bayyana damuwa kan yadda matasa a jihar Kano ke mayar da magungunan wasu cututtuka a matsayin ababen sanya maye.
Kungiyar tuntuba ta dattawan Arewa ACF, ta koka kan yadda ba’a zartar da hukuncin da ya kamata kan mutanen da ke da hannu akan matsalolin satar yara da akan yi safarar su daga yankin arewacin Najeriya zuwa kudanci domin sayar da su.
Masana tattalin arziki sun ce samame da jami'an hukumar EFCC su ka kai shalkwatar rukunin kamfanonin Dangote a Legas, a ranar Alhamis, ka iya shafar farashin hannayen jari na kamfanonin, amma ba zai shafi hada hadar sarrafawa da kuma farashin kayayyakin na Dangote ba a kasuwannin duniya.
Yayin da Kotun Kolin Najeriya ta ce nan gaba kadan zatayi zaman sanar da hukuncin ta akan shari'ar kujerar gwamnan Kano, Rundunar 'Yan Sandan jihar ta nemi hadin kan kafofin yada labarai domin tabbatar da zaman lafiya da doka da oda a fadin jihar, gabani da kuma bayan sanar da hukuncin.
Batun takaddama tsakanin shugabannin kungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma, ECOWAS, da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tnubu ke jagoranta da shugabannin mulkin soja a Jamhuriyar Nijar na ci gaba da daukar hankalin masana da masu fashin bakin kan sha’anin siyasa da diflomasiyya.
Domin Kari