Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babbar Kotun Tarayya Dake Kano Ta Ce Ta Na Da Hurumin Sauraron Shari'ar Takaddamar Masarautar Kano


Masarautar Kano
Masarautar Kano

Babbar kotun tarayya dake Kano ta ce ta gamsu da hujjojin ta masu kara suka gabatar, saboda haka tana da hurumin sauraron shari'ar takaddamar sarautar Kano.

Alhaji Aminu Babba Danagundi, Sarkin Dawaki Mai Tuta kuma guda cikin masu nadir sarki a masarautar Kano ne ya shigar ta kara yana kalubalantar rushe sarautu hudu na Kano da kuma sauke sarakuna guda biyar na jihar Kano.

A zaman kotun na yau karkashin jagorancin Mai Sharia M.A Liman yace kotun ta gamsu da hujjar da lauyan Babba Danagundi cewa, matakin Majalisar Dokokin Kano dana gwamnatin jihar Kano game da sauke sarakunan ya ci karo da yancin sa.

Masarautar Kano
Masarautar Kano

Yace bisa laakari da haka kotun nada hurumi game da duk wani al'amari da ya shafi tauye hakkin dan kasa a kowane lamari.

Yanzu abin da ya rage shine kotu ta ci gaba da sauraron karar.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG