A ranar Alhamis ne kamfanin American Express ya kaddamar da katin lamuni na kudin dala a birnin Lagos, a wani mataki na saukaka wa ‘yan Najeriya musamman ‘yan kasuwa a harkokinsu da ke da alaka da kudaden ketare na dala.
Dr. Lawan Habib Yahya, masanin tattalin arziki ne a Najeriya, yayi karin bayani dangane da alakar wannan katin na lamunin kudin dala da kuma darajar takardun kudin Najeriya na Naira.
“Idan bukatun neman musayar kudaden ketare na dala suka ragu daga kamfanoni da daidaikun mutane, saboda suna samun wadannan kudade ta hanyar katin lamuni daga kamfanin American Express Credit Card, to babu shakka darajar naira na iya karuwa saboda dama yawaitar bukatun kudin dalar ne ke daga farashinta,” a cewar Dr. Lawan.
Da alama dai masu masana’antu a Najeriya sun yi maraba da wannan yunkuri na kaddamar da katin lamuni na kudin dala a Najeriya, kamar yadda Alhaji Sani Hussaini Sale, mamba a kwamitin koli na kungiyar masu masana’antu ta Najeriya (MAN), kuma mataimakin shugaban cibiyar kula da harkokin kasuwanci, masana’antu, ma’adinai, da ayyukan noma ta jihar Kano (KACCIMA) ya bayyana.
“Dama kokawar cinikayya da kasashen waje ta zama da wahala saboda dalar na neman ta tada hankali, amma zuwan wannan tsari na katin bada lamuni na kudin dala zai magance kalubalen, musamman yadda idan aka baka kudi daga dala dubu daya zuwa dubu 20 zasu taimaka sosai, a cewar Alhaji Sani.
Ya kuma ce “Fatan mu shi ne wannan kamfani na American Express credit Card ya iso Kano a arewacin Najeriya, don mu hada hannu da shi a cibiyarmu. Zamu sada shi da ‘yan kasuwa domin wayar da kansu game da alfanun wannan tsari daya zo dashi”.
Amma a cewar, Dr. Lawan Habib Yahya, akwai bambanci a tsakanin katin lamuni na American Express Credit Card da kudaden Crypto da ake hada hadarsu a kafar zamani ta Intanet.
“Shi kudin Crypto kudi ne da ake juya shi ta kafar sadarwa ta Intanet, ba kudi ne lakadan ba, amma shi American Express Credit Card kudi ne lakadan za’a saka maka a katinka kuma ka yi sayayya ko cinikayya da shi a kasashen waje, kamar yadda zaka yi amfani da katinka na bankin Najeriya takardun kudi na naira su fita,” inji Dr. Lawan.
Baya ga Najeriya, kamfanin American Express ya ce yana da burin fadada wannan tsari na katin lamunin kudin dala zuwa sauran kasashen Afrika kamar su Rwanda da Ghana.
Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:
Dandalin Mu Tattauna