Ko wace shekara a lokacin aikin hajji akan fuskanci matsaloli da dama inda ko wace shekara ake ganin wasu kalubale na daban dake kara bijirowa.
Alhazan Najeriya 13 ne suka rasa ransu ya yin gudanar da aikin hajjin bana na shekarar 1444 bayan hijara wanda yayi daidai da shekarar 2023 miladiyya.
Birnin Makka mai daraja ya karbi bakunci dubban mutane daga kasashe dabam-daban na fadin duniya don gudanar da aikin Hajjin bana na hijira ta 1444, wanda yayi daidai da shekarar 2023 miladiyya.
Jami’an Hukumomin Alhazai sun garzaya zuwa Mina, Arfa da Muzdalifa don tabbatar da komai na tafiya daidai gabanin fara aikin Hajjin nan da sati guda.
Shugaban ofishin kula da harkokin alhazai da ke Madina Ibrahim Idris Mahmud ya shaida wa Sashen Hausa na Muryar Amurka cewa suna gudanar da ayyukansu na jigilar maniyyata zuwa kasa mai tsarki kamar yadda suka tsara.
Hajjin Bana wanda ya zo da wasu sauye-sauye sakamakon rikicin Sudan da ya sanya aka rufe sararin samamniyar kasar da ya tilasta bin wasu hanyoyi tare da karawa tafiyar nisa, ka iya haifar da barazana ga lafiyar Maniyata.
Rikicin Sudan da ya sa aka rufe sararin samaniya ya janyo karin kudin kujerar aikin Hajji a Najeriya da dala 250, don dole a zagaya ta hanya mai nisa da hakan ya sa kamfanonin jiragen da za su yi jigilar maniyyatan suka bukaci karin kudi.
Batun tabarbarewar tsaro da kuma kuncin tattalin arziki su ka fi zama abubuwan tattaunawa a tsakanin ‘yan Najeriya musamman talakawa kan mulkin shugaba Buhari na shekaru 8.
Biyo bayan biris da gwamnatin Najeriya tayi na barazanar shiga yajin aiki da Kungiyar likitoci masu neman kwarewa NARD ta yi sati biyu da suka gabata, idan har gwamanti ba ta biya musu bukatunsu da hakkokinsu ba, kungiyar likitocin ta tsunduma yajin aikin gargadi na kwanaki biyar.
Domin Kari