Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alhazai Za Su Iya Fuskantar Matsalar Daskarewar Jini Sakamakon Zama Mai Tsawo A Cikin Jirgi


Wasu Alhazai masu tafiyan aikin hajji
Wasu Alhazai masu tafiyan aikin hajji

Hajjin Bana wanda ya zo da wasu sauye-sauye sakamakon rikicin Sudan da ya sanya aka rufe sararin samamniyar kasar da ya tilasta bin wasu hanyoyi tare da karawa tafiyar nisa, ka iya haifar da barazana ga lafiyar Maniyata.

ABUJA, NIGERIA - Wani bincken kimiyya da aka gudanar ya nuna cewa idan mutum ya wuce awa 4 a cikin jirgi musamman wanda shekarun sa suka haura 50 daya a mutum dari shida zai iya fuskantar matsalar daskarewar jini da ake kira da Deep Venus Thrombosis a turance.

Hakan fito ne daga bakin Jami’i a ma’aikatar lafiya ta Najeriya kuma shugaban likitoci dake kula da maniyata a Hukumar Alhazai ta kasar(NAHCON) Dakta Sa’idu Ahmad Dumbulwa a lokacin ya yake zantawa da Saashen Hausa na VOA.

Dakta Sa’idu Ahmad yace hakan yasa suka bullo sabbin hanyayi da kuma shawarwari da dasu taimaka wajen tabbatar da lafiya maniyatan.

Hanyoyin sun hada da Sanin tarihin lafiyar maniyata musamman ‘yan sama da shewkara 50, Saka kaya da takalma wadanda basu da matsi, tabbatar da cewa akawai ma’aikatan lafiya a jiragen dake jigilar maniyata, da kuma hada gwiwa da ma’aikan jirgin don tsarin wajen zama da tabbatar da akwai duk wasu magungunan da ake bukata a cikin jirgi.

Alhazan Najeriya
Alhazan Najeriya

Dr. Sa’id ya kara da cewa sun kuma dauki mataki na wayar da kan Maniyatan a harshen Hausa, Turance, Yoruba da kuma Pigin kan irin matakan daya kamata su dauka don kare aukuwar wannan matsala da suka hada da motsa jiki a cikin jirgi bayan zaman akalla awa biyu.

Idan dai za’a iya tunawa an fara jigilar Alhazai a Najeriya zuwa kasa mai tsarki ne a ranar 25 ga watan Jiya, kawo yanzu akalla mutum 30,000 ne suka isa kasar saudiyya.

Saurari cikakken rahoto daga Hauwa Umar:

Alhazai Za Su Iya Fuskantar Matsalar Daskarewar Jini Sakamakon Zama Mai Tsawo A Cikin Jirgi.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG