Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

HAJJ 2023: NAHCON Za Ta Hukunta  Jihohin Da Su ka Kyale Masu Juna Biyu Zuwa Aikin Hajji


Wasu mata masu juna biyu a hajji
Wasu mata masu juna biyu a hajji

Ko wace shekara a lokacin aikin hajji akan fuskanci matsaloli da dama inda ko wace shekara ake ganin wasu kalubale na daban dake kara bijirowa.

A bana an fuskanci kalubale da suka hada da zafin rana, samun mata masu juna biyu, karancin wayar da kan Alhazai, yawan Jama’a ko cunkoso da ya haifar da rashin tsafta wanda hakan ya zama tamkar taki ne wajen yaduwar cuta.

Hakan ya fito ne daga bakin kwamishinan ma’aikatar lafiya ta Najeriya kuma shugaban da ke kula da dukkan lamuran da suka shafi lafiyar Alhazai Dakta Sa’idu Ahmad Dumbulwa a zantawarsa da VOA Hausa a ofishinsa dake Ummul Jood a Makkah, bayan kammala ziyarar gani da ido na yadda likitocin da ke kula da alhazai suke gudanar da aikin su.

Wasu Alhazai masu tafiyan aikin hajji
Wasu Alhazai masu tafiyan aikin hajji

Kwamishinan yace sunyi la’akari da cewa akwai kimanin tsofaffi dubu 15 yan shekara 60 zuwa sama da suka gudanar da aikin hajjin bana kuma sun sami matsalar ciwon kafa da ta jiki bayan kammala aikin wanda hakan yasa suka bukaci bude wasu asibitoci don basu magani da kuma tabbatar da cewa likitocin suna kula da su yadda ya kamata.

Dr. Saidu ya kuma ce hukumar alhazai ta Najeriya NAHCON da kuma kwamitin kula da lafiyar Alhazai ba za su lamunci dokar da jihojhi ke sabawa ba na bari mata masu juna biyu suna zuwa aikin hajji, inda ya ce za su dauki matakin hukunta duk wanda ya saba dokar wajen cin sa tara.

Daga karshe Dr. Sa’idu yace duk da cewa an sami wadanda suka sami matsalar rashin lafiyar kwakwalwa wanda yawancin su sakamakon rudewa ko rikicewa ne, amma likitoci sun yi kokari wajen ba su magani kuma sun sami lafiya.

Saurari rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG